Home / Kasuwanci / Za A Inganta Kasuwar Duniya Ta Kaduna – Sarkin Zazzau

Za A Inganta Kasuwar Duniya Ta Kaduna – Sarkin Zazzau

 Imrana Abdullahi
Mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya bayyana cewa da ikon Allah zai tabbatar da an inganta Kasuwar duniya ta kasa da Kasa da ke Kaduna.
Mai martaba Sarkin Zazzau ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi wajen taron rufe kasuwar duniya ta wannan shekarar da aka yi tsawon kwanaki Goma.
Sarkin ya ce kasuwar duniya na da matukar muhimmanci kwarai wajen bunkasa tattalin arzikin Jihar baki daya.
Mai martaban ya kuma bayyana cewa matsalar da cutar Korona ta haifar lamari ne da ya shafi wurare da dama a duniya don haka ba Jihar Kaduna ba ce kadai kuma da ikon Allah lamarin zai wuce kamar ba a ta ba yinsa ba.
Jama’a da dama ne suka gabatar da jawabai a wajen taron rufe kasuwar.
An kuma bayar da kyaututtuka ga kamfanoni,ma’aikatun Gwamnati da yan kasuwar da suka yi fice sakamakon halartar kasuwar ta ba na.
An fara cin kasuwar lafiya an kammala lafiya kowa na murna tare da son barka.

About andiya

Check Also

Za Mu Kakkabe Yan Ta’adda, Bola Tinubu Ya Tabbatarwa Gwamna Dauda Lawal Na Zamfara

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatin sa na kawo ƙarshen matsalar ’yan …

Leave a Reply

Your email address will not be published.