Home / Kasuwanci / Shugaban Kungiyar Katsinawa da Daurawa Na Kasa Ya Kai Ziyarar Jaje Ga Yan Kasuwar Sakkwato

Shugaban Kungiyar Katsinawa da Daurawa Na Kasa Ya Kai Ziyarar Jaje Ga Yan Kasuwar Sakkwato

Shugaban Kungiyar Katsinawa da Daurawa Na Kasa Ya Kai Ziyarar Jaje Ga Yan Kasuwar Sakkwato

Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban kungiyar Katsinawa da Daurawa na kasa Alhaji Aliyu Daura ya kai ziyarar jajantawa yan kasuwar Sakkwato sakamakon matsalar Gobarar da ta tashi a kasuwar da ta haifar da asarar dukiya mai dimbin yawa.
Alhaji Aliyu Daura ya kai wanann ziyarar jaje ne tare da shugaban cibiyar yan kasuwa da masana’antu na Jihar Sakkwato Alhaji Bello Maiwurno da kuma mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Mannir Dan’iya.
Alhaji Aliyu Daura ya zagaya wurin da Gobarar ta cinye inda ya ganewa idanunsa tare da yin addu’ar Allah ya kiyaye faruwar irin wannan matsalar ya kuma mayarwa yan kasuwar asarar da suka yi.
Shugaban kungiyar katsinawa da Daurawa na kasa Alhaji Aliyu Daura yake zagayawa lokacin da ya kai ziyarar jaje
Ya kuma yi addu’ar samun kariya ubangiji, zaman lafiya da kuma karuwar arziki ga yan Nijeriya baki daya.
A nasa jawabin a lokacin ziyarar mataimakin Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Mannir Dan, iya godiya ya yi wa daukacin yayan kungiyar inda ya karfafa masu Gwiwa da cewa Gwamnatin a shirye take domin taimakawa kungiyar a duk lokacin da hakan ta taso.
Ya kuma bayar da shawara cewa a ci gaba da yin addu’ar neman zaman lafiya da dai- daituwar al’amura a kasa baki daya.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.