Home / MUKALA / BOLA AHMED TINUBU NAGARI NA KOWA

BOLA AHMED TINUBU NAGARI NA KOWA

 

 

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI

 

Sakamakon irin shauki na Zakuwa da kosawar da dimbin al’ummar Najeriya suka yi domin ganin Nagari na kowa da ake yi wa lakabi da Inuwa baki kyamar kowa wato cikakken dan kishin kasa Dokta Bola Ahmad Tinubu, wanda ya yi an gani musamman lokacin da ya zama Gwamnan Jihar Legas na tsawon shekaru Takwas inda ya kawo wa Jihar da ma Najeriya ci gaban da a yau ake tutiya kasancewa kowa na alfahari da shi.

 

 

Kamar yadda kowa ya Sani a wannan lokacin da Bola Ahmad Tinubu, na Gwamnan Jihar Legas ya yi kokari kwarai ya mayar da Jihar mai dogaro da kanta musamman ta fuskar tara kudin shiga da sauran yanayin ci gaban kasa baki daya.

 

 

Wannan yanayi da ya mayar da Jihar Legas ta Sanya har a kwanan Gobe Jihar ta zama ta daya wajen lamarin dogaro da kanta, inda kusan duk lokacin da za a yi misalin Jihohin da za su iya rike kansu babu wata tantama ana yin misali ne da Jihar Legas wadda babu wata shakka za ta iya dogara da kanta.

 

 

Saboda a lokacin da Dokta Bola Ahmad Tinibu, na matsayin Gwamnan Jihar Legas, ta zamo Jihar da ke iya biyan Albashi ba tare da sai an jira kudin dauni daga Gwamnatin tarayya b, wanda a tsari irin na tafiyar da Gwamnati hakan al’amari ne mai girma da ya zama abin ayi koyi a kuma yaba da shi a koda yaushe.

 

 

Kuma wani babban al’amarin da kowa zai iya yin tunkaho da shi a nan kuma shi ne irin yadda duk wanda ya kusanci wannan bawan Allah Dokta Bola Ahmad Tinubu, sai bayar da shaida ta gaskiya cewa hannunsa a bude yake sakamakon irin yadda yake rungumar kowa ba tare da nuna wani bambanci ba, wannan hali na mutum ya kasance hannunsa a bude ma’ana mai yawan yin kyauta da kuma taimakawa jama’ar da ke matukar bukatar hakan hali ne da ya yi dai – dai da karantarwar addini musulunci saboda kamar yadda ya zo a musulunce hannun da ya kasance a sama ya fi na kasa, wato mai kyauta ya fi wanda ke tarba hannunsa Garba bashi, kuma akwai wani karin magana ma a hanusa da ke cewa mai kyauta surukin mai karba.

 

 

Hakan ta Sanya a wani taron da aka yi a duniya na kasa da kasa aka tabbatar da cewa hakika ya samu maki kashi sama da Saba’in saga cikin dari na zama wani mutumin da ya yi sanadiyyar dimbin jama’ar da ba a san adadinsu ba suka zama wani abu a duniya.

 

 

Bisa wannan yar gajeriyar shimfidar ne nake ganin hakan ya sa wadansu dubban kungiyoyin matasa da kuma wasu masu gudanar da ayyuka a domin inganta rayuwar al’umma ya sa suka yi wani gangami a garin Abuja ranar Litinin din nan da ta gabata inda suka taru a babban dakin taro na kasa da kasa da ke Abuja suka yi taron kwana daya domin a wayarwa da daruruwan yayan kungiyoyi da dama da suka taru kai, a kan yadda za su bi jama’a Gida Gida, lungu da sako na dukkan birane da kauyukan da ke Najeriya su jawo hankulan jama’a game da farko ma me ake nufi da Bola Ahmad Tinubu ya yake kuma ya alkairinsa yake? Me ya yi a rayuwarsa kuma me zai iya aiwatarwa domin Najeriya da yan kasa su samu ci gaba? duk a cikin fahimtar Juna wanda hakan su suka ga ya dace su aiwatar da hakan saboda yan magana na cewa yana kyauta tukwuici kuma in baka iya kyauta ba ka ba mai baka.

 

A wajen wannan taro dai mai gayya mai aiki uban wannan tafiya Sanata Abu Ibrahim Dattijo ka yi taka ka yi ta mai karamin karfi, kamar dai irin yadda mutanen yankin Karaduwa a Jihar Katsina suke yi masa kirari Abu na Abuja mai abin bayarwa ya fadakar kuma ya ja hankalin jama’a kan cewa su Sani wannan taro ba na gangamin tsayar da Dokta Bola Ahmad Tinubu, takara ba ne domin hukumar zabe ba ta ma ko bayar da izini ko yin wani jawabi mai kama da hakan ba.

 

 

Sanata Abu Ibrahim ya ci gaba da cewa taro ne na daruruwan kungiyoyi masu mambobi dimbi da yawan gaske a ko’ina a fadin Najeriya Saboda aje a ci gaba da fadakar da jama’a game da irin alkairi da nagartar Dokta Bola Ahmad Tinubu, wanda cikin yardar Allah idan ya zama shugaban kasa zai zamowa kowa alkairi domin daman can da abin arziki da alkairi aka san shi kuma har gobe ya na nan a kan hakan.

 

 

Mutane irin su Honarabul Abdulmumini Jibrin daga Jihar Kano wanda shi ne maga isar wannan tafiya da yake jagorantar tafiyar Support Group Management Council (SGMC) da ya yi bayanin irin yadda muhimmancin fadakar da jama’a da kuma aikin sa kai yake a can ga al’umma na can kasa domin a samu kwalliya ta biya kudin sabulu.

 

 

Abdulmumini Jibrin ya kuma yi wa taron dimbin jama’ar da suka taru a wannan waje irin bukatar da ke da akwai wajen ninka goyon baya da hadin kai da ake ba shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bukata ta biya nufi.

 

 

Ya ce san irin hadin kai da goyon bayan da ake ba shugaban kasa Mihammadu Buhari, amma ya ninka a kara ninkawa.

 

 

Taron dai ya samu halartar dimbin jama’a masu rajin dabbaka ci gaban tattalin arzikin kasa da kuma fadakarwa game da Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.

 

 

Inda muka yi kicibis da matasan kungiyar Kiristoci ta Najeriya wato kwararru a fannoni daban daban da suka jaddada hadin kansu da goyon bayansu ga wannan tafiya ta Asiwaju Bola Ahmad Tinubu da suke tabbatar mana cewa kwalliya za ta biya kudin sabulu idan ya zama shugaban Najeriya.

 

 

Mustapha Imrana Abdullahi ne ya rubuta wannan makalar 080 3606 5909 or email- shieldg2014@gmail.com

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.