Home / News / BOLA TINUBU NE DAN SIYASAR DA YA YI KARKO TAURARUWARSA KE HASKAWA A KULLUM 

BOLA TINUBU NE DAN SIYASAR DA YA YI KARKO TAURARUWARSA KE HASKAWA A KULLUM 

MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI
An bayyana shahararren dan siyasar tarayyar Najeriya Bola Ahmad Tinubu a matsayin mutumin da ya fi duk wani dan siyasa karko tun bayan da ya sauka Gwamnan Jihar Legas, amma tauraruwarsa ke kara haske a koda yaushe.
Dan jarida Ali M Ali ne ya bayyana hakan lokacin da yake tattaunawa da kafar Talbijin ta Kaftan hausa da ke da babban ofishinsu a Abuja.
Ali M Ali ya ce idan za a yi tuba na musamman kuma a tsanake mutum zai ga cewa babu wani dan siyasar da ya yi karko tun da ya sauka daga Gwamnan Jihar Legas ” babu abin da Bola Tinubu ke yi sai kafa mutane a matakai daban daban wanda hakan ya Sanya ya zama mutumin da ke da ruwa da tsaki a kusan ko’ina a fagen siyasa da matakin Gwamnatin tarayya”.
Ali M Ali ya kara da cewa sakamakon kokari da kwazon aiki na dan siyasa Bola Ahmad Tinubu ya sa a lokacin da yake Gwamnan Jihar Legas tattalin arzikin Jihar ya inganta har ta kai Jihar ta tsaya da kafafunta har kananan hukumomi suka samu damar zama da kansu a lokacin mulkin Obasanjo.
” A lokacin da Bola Tinubu na Gwamnan Jihar Legas ya kirkiri kananan hukumomi sai shugaban Najeriya na wancan lokaci Obasanjo ya hana aba kananan hukumomin Legas kudi amma sakamakon kokari da jajircewa Bola Tinubu duk ya ci gaba da rike kananan hukumomin, kuma sai da tattalin arzikin Jihar Legas ya kasance tamkar tattalin arzikin wasu kasashen Afrika da yawa da a kididdiga ake bayanin cewa ya kai na kasashe a kalla biyar duk kuma sakamakon jajircewar Bola Ahmad Tinubu ne da kwarewar aiki”.
Kuma wani babban abin duba wa a halin yanzu shi ne tauraruwar Bola Tinubu ce ke haskawa a fagen siyasar Najeriya don haka ake ganin ya na da damar dare shugabancin mulkin kasar nan.

About andiya

Check Also

PRESIDENT TINUBU COMMENDS DANGOTE GROUP OVER NEW GANTRY PRICE OF DIESEL

  President Bola Tinubu commends the enterprising feat of Dangote Oil and Gas Limited in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.