Home / Labarai / BOLA TINUBU NE YA LASHE ZABEN SHUGABAN KASA

BOLA TINUBU NE YA LASHE ZABEN SHUGABAN KASA

…..HUKUMAR ZABE TA BAYYANA BOLA TINUBU A MATSAYIN WANDA YA LASHE ZABEN SHUGABAN KASA
Daga Imrana Abdullahi
Bayanan da ke fitowa daga babban birnin tarayya Abuja na cewa shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa Farfesa Mahmud Yakubu ya tabbatar da Bola Ahmad Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.
Inda ya kayar da dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.

Bola Ahmad Tinubu dai ya samu nasara ne a kan sauran yan takarar da suka fafata da shi su Goma sha Bakwai 17

Tinubu ya samu yawan kuri’u miliyan 8,794,726, sai kuma Atiku Abubakar ya samu kuri’u miliyan 6,984,520.

Bola Ahmed Tinubu ya yi wa jama’a kwarya kwaryan jawabi inda ya ce wannan matsayi na shugaban kasa da Allah ya bashi da cewa wani gagarumin aiki ne na yi wa kasa hidima don haka “ni kamar yaron mota ne”.

Zamu kawo maku yadda lamarin yake nan gaba.

.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.