Home / Labarai / AN YABAWA YAN NIJAR MAZAUNAN NAJERIYA

AN YABAWA YAN NIJAR MAZAUNAN NAJERIYA

Dokta Aminatou Abdoulkarim Muhammad, ta yaba tare da yin godiya ga daukacin al’ummar Nijar mazauna Najeriya bisa irin kokarin da suka nuna na kin shiga harkar zabe a lokacin gudanar da zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya da na Dattawa da ya gudana a duk fadin kasar.

Dokta Aminatou ta ci gaba da cewa hakika dole ne a yaba wa daukacin mutane yan Nijar da ke zaune a tarayyar Najeriya bisa irin kishin kasa da jin magana da suka yi na rashin shiga cikin harkar zaben da aka yi domin jama’ar kasar su zabi shugaban kasa da mataimakinsa tare da yan majalisun dokokin tarayya da na Dattawa.

Hakika kunyi abin da ya dace da haka ne nake yin godiya da kuma addu’ar Allah ya saka ma kowa da alkairi ya kuma hada kawunan mu, kuma muna fatan kamar yadda aka yi lafiya aka kammala zaben lafiya Allah ya kara hada kawunanmu da alkairi. Muna yin addu’a Allah ya kara mana zaman lafiya da hadin kai a tsakanin mu da wannan ne nake kara mika godiya ta a gare ku mutanen Nijar mazaunan Najeriya bisa irin yadda kuke nuna sanin yakamata a koda yaushe”.

“Muna kuma fatan cewa yadda aka yi zaben shugaban kasa lafiya aka kammala lafiya, muna fata da yin addu’ar Allah yasa ayi zaben Gwamna, mataimakansu da zaben yan majalisun Jiha ayi lafiya a kammala lafiya. Allah ya tabbatar da alkairi, hakika muna godiya kwarai da hadin kan da ake yi tare da natsuwa da yin mu’amalla mai kyau da mutanen Najeriya.

Dokta Aminatou Abdoulkarim ta kara da cewa ana jan kunnen mutanen Nijar mazaunan Najeriya a kan yadda aka yi zaben da ya gabata ba a samu wani rahoton wanda ya Sanya hannunsa a cikin lamarin zaben Najeriya ba haka ana fatan kada wani ya Sanya kansa a duk zabukan da za a yi a nan gaba, muna fatan ganin an gudanar da zaben da ke tafe lafiya a kammala shi lafiya, muna kara yin godiya a gare ku”.

About andiya

Check Also

DOLE SAI MUN SANYA FASAHAR ZAMANI DON YAƘI DA MATSALAR TSARO -GWAMNA LAWAL GA MAJALISAR ƊINKIN DUNIYA

  Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada buƙatar amfani da manyan na’urorin zamani domin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.