Home / Kasashen Waje / BOLA TINUBU YA TA FI KASAR FARANSA

BOLA TINUBU YA TA FI KASAR FARANSA

Daga Imrana Abdullahi

Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tashi zuwa birnin Paris domin halartar taron shugabannin kasashen duniya a birnin Paris na kasar Faransa, domin yin nazari tare da rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya ta hada-hadar kudi ta duniya wadda ta sanya kasashe masu rauni a jerin fifikon tallafi da saka hannun jari, biyo bayan mummunan tasirin sauyin yanayi, matsalar makamashi.  da cutar Korona.

Da safiyar yau ne ya dauki jirgi mai saukar ungulu daga fadar shugaban kasa zuwa filin tashi da saukar jiragen sama na kasa da kasa Nnamdi Azikwe, da ke Abuja inda gwamnonin jihohi, jami’an gwamnati, da sojoji suka tarbe shi.

A cikin wata sanarwa da Dele Alake, mai ba da shawara na musamman, ayyuka na musamman, sadarwa, da dabaru ya fitar a ranar Litinin, shugaban zai halarci taron na kwanaki biyu a ranakun 22 da 23 ga watan Yuni, wanda zai yi la’akari da damar da za a maido da sararin hada-hadar kudi ga kasashen da ke fama da matsananciyar wahala.

Ya ci gaba da bayyana cewa, Shugaba Tinubu da sauran shugabannin duniya, da cibiyoyi da dama, da masana harkokin kudi, da masana tattalin arziki, za su dauki hanyar da ta dace wajen farfado da tattalin arzikin kasar daga annobar Korona da tabarbarewar tattalin arziki, da nufin samar da hanyoyin samun kudi,  da zuba jari da za su yi amfani da ci gaba.

Kamar dai yadda sanarwar ta ce Shugaban zai dawo ne a ranar Asabar, tare da rakiyar mambobin kwamitin ba da shawara kan manufofin shugaban kasa tare da wasu jami’an Gwamnati.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.