Home / News / BOLA TINUBU YA TAIMAKAWA BUHARI DA ATIKU – ABU IBRAHIM

BOLA TINUBU YA TAIMAKAWA BUHARI DA ATIKU – ABU IBRAHIM

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Sanata Abu Ibrahim daga Jihar Katsina ya bayyana cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dade ya na taimakawa al’ummar arewacin Najeriya a fannin siyasa da sauran al’amuran tafiyar da rayuwa da dama.
Abu Ibrahim ya bayyana hakan ne a wani faifan bidiyon da aka yada a kafafen Sada zumuntar yanar Gizo.
” Karin shekarar 2015, lokacin da Muhammadu Buhari ya yi takara har sai uku babu lokacin da ya samu yawan kuri’ar da ta kai kashi 25 a yankin Kudu maso Yamma, amma a lokacin da Bola Tinubu ya shiga cikin lamarin hidimar siyasar Buhari sai da ya samu kuri’a kashi 25 a kowace Jiha ta yankin Kudu maso Yamma”.
Hakazalika Bola Tinubu ya taimakawa Atiku Abubakar lokacin da ya yi takarar shugaba kasa, don haka tun da dadewa Bola Tinubu ya dade ya na taimakawa yan arewacin Najeriya a harkar siyasa da kuma sauran fannoni da dama na rayuwar duniya kuma sun amfana kwarai.
Saboda haka ba wani sabon al’amari ba ne ga dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu ta fuskar taimakon yan arewacin Najeriya domin ya saba tun da dadewa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.