Home / Labarai / Buhari Ya Dakatar Da Shugaban NBC, Modibbo

Buhari Ya Dakatar Da Shugaban NBC, Modibbo

Imrana Abdullahi

Shugaban tarayyar Nijeriya Muhammadu Buhari, ya dakatar da Darakta Janar na hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa Ishaq Modibbo Kawu, daga Ofis.

Dakatarwar da tashar Talbijin ta AIT ta yada a ranar Juma’a, ta fara ne nan take kuma tana da dangantaka da batun cin hanci da karbar rashawa da hukumar ICPC ta ce ya rutsa da shi da kamafanin sadarwa na Pinnacle, domin yin aikin zamanantar da signa a babban birnin tarayya Abuja.

Laifin da ake batu tsakanin Modibbo da kamfanin sadarwa na Pinnacle, tana hannun hukumar yaki da batun cin hanci da rashawa da abin da ya jibanci hakan ta ICPC, da ake zarginsu da badakalar naira miliyan 2.5.

Batun dakatarwar da aka yi wa Modibbo da Buhari ya yi hukumar ICPC ce ta bukaci hakan domin kammala binciken da suke yi har sai sun gama kaf.

Kafar yada labarai ta AIT ta ruwaito cewa tuni aka umarci ma aikacin da ya fi girman mukami da ake kira Furofesa Armstrong Idachaba, da ya rike aikin tafiyar da hukumar

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.