Home / News / An Sanya Dokar Hana Fita Ta Kwana Uku A Bayelsa

An Sanya Dokar Hana Fita Ta Kwana Uku A Bayelsa

Jami’an tsaron yan sanda a Jihar Bayelsa karkashin jagorancin Uche Anozia ta bayyana cewa sun sa dokar hana fitar ne sakamakon irin yadda tashin tashina ta barke a babban birnin Jihar na Yenagoa jim kadan bayan Dauye Diri na PDP ya karbi takardar lashe zabe daga hukumar zabe ta INEC. kuma aka rantsar da shi.
Tarzomar dai ta barke ne tun bayan da hukumar zabe ta mikawa dan PDP Daiye Diri takardar lashe zabe a matsayin Gwamnan Jihar Bayelsa, lamarin da bai yi wa yayan Jam’iyyar APC dadi ba
Tun bayan da kotun kolin Nijeriya da ta yanke hukuncin cewa an samu matsala a takardun dan takarar mataimakin Gwamnan Jihar Bayelsa karkashin APC wanda suka tsaya tare da mai takarar Gwamnan APC da hukumar zabe ta bayyana David Lyon ya lashe zaben Gwamnan a kwanan baya da aka yi zaben Gwamna.
An dai sa dokar ne daga karfe 8 :00 na Yamma zuwa karfe 6:00 na safe na tsawon kwarai uku daga yau Juma a zuwa ranar Lahadi mai zuwa.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.