Home / KUNGIYOYI / Buhari Ya San Me Ke Kawo Cin Hamci Da Rashawa – Batayya

Buhari Ya San Me Ke Kawo Cin Hamci Da Rashawa – Batayya

Mustapha Imrana Abdullahi
An yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya tabbatar da gudanar da binciken me ke kawo cin hanci da rashawa.
Shugaban kungiyar masu motocin sufuri ta kasa Dokta Kasim Ibrahim Batayya ne ya yi wannan kiran lokacin da yake tattaunawa da kafar yada labarai ta NTA hausa.
Batayya ya bayyana cewa babban al’amarin da ya dace shugaba Buhari ya kula da shi ne abin da ke kawo cin hanci da karbar rashawa.
“Idan shugaban kasa ya tabbatar da gano abin da ke kawo cin hanci da rashawa za a samu hanyar magance matsalar”, inji Kasim Batayya.
Sai dai ya jinjina wa shugaba Buhari a kan batun inganta harkokin sufurin Jirgin kasa, wanda ya ce zai taimakawa harkar sufuri kwarai.
Ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su rika amincewa da yin kuskure domin samun yadda za a samar da yin gyara
“Hakika muna da taswirar dukkannin titunan Jihohin kasar nan wanda dalilin hakan ya haifar da samun nakasun rashin fadada tituna duk da irin yadda jama’a ke kara yawa a Najeriya baki daya.
Babu wata jiha da ke da ingantaccen ofishin VIO, wasu kuma sun kashe ofisoshin VIO an mayar da shi wani abu daban sabanin yadda lamarin aka san shi tun farko

About andiya

Check Also

Our Mandate Is To Organise Congresses, Says Labour Party Transition Committee Chairman, Umar

  Former president of the Nigerian Labour Congress, NLC, and Transition Committee chairman of the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.