Home / Labarai / Buni Ya Jajantawa Wadanda Gobarar Kasuwar Bayan-Tasha Ta Yiwa Barna

Buni Ya Jajantawa Wadanda Gobarar Kasuwar Bayan-Tasha Ta Yiwa Barna

 

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

 

Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya bayyana matukar bakin cikinsa game da jin labarin afkuwar gobara da ta afku a kasuwar Bayan-Tasha (kasuwar Dubai) a daren ranar Jumu’a.

A wata sanarwar manema labarai dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mamman Mohammed, Gwamnan ya bayyana hakan a matsayin wani babban koma baya  ga tattalin arziki da kuma babban rashi ga daidaikun masu shi da ma jihar baki daya.

“Na yi matukar bakin ciki da wannan bala’in da ya shafi rayuwar mutane da yawa da iyalan su wadda kuma iftila’i ne daga Allah SWT.”

“Gwamnati za ta duba wannan babban lamari domin bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa domin su sake tsayawa kan kafafunsu.

“Ba da jimawa ba za a kebe Kasuwan Zamani na Damaturu, Gashua da Nguru  don ‘yan kasuwa su koma cikin yanayi mai kyau da tsaro, don a kare su daga barazanar barkewar gobarar da ke faruwa  a kasuwannin,” in ji Gwamna Buni.

An gina sabbin kasuwannin zamani da fasahar hana gobara tasiri ta amfani da konannun bulo domin kare kaya daga barkewar gobara.

Gwamnan ya yi kira ga ‘yan kasuwa da sauran jama’a da su rika daukar matakan kariya a kodayaushe domin guje wa gurbacewar wutar lantarki da sauran hanyoyin da za su iya haifar da gobara a wuraren kasuwanci.

About andiya

Check Also

Backward Integration: Dangote Targets 700,000MT of Refined Sugar in Four years

As Q1 revenue rise by 20.1% to N122.7bn   Dangote Sugar Refinery Plc (DSR) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.