Home / Labarai / Gwamnatin Jihar Katsina Ta Soke Duk Wani Filin Da Aka Bayar Ba Bisa Ka’ida Ba

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Soke Duk Wani Filin Da Aka Bayar Ba Bisa Ka’ida Ba

Daga Imrana Abdullahi

A cikin wata sanarwar da Gwamnatin Jihar Katsina ta fitar daga ofishin shugaban ma’aikata dauke da sa hannun Ado Yahaya,Daraktan kula da harkokin al’umma, sanarwar na dauke da kwanan wata ranar 6 ga watan Yuni, kuma mai dauke da lamba kamar haka 6/June/2023 da lamba KTS/HOS/S/70/VOLIII/400 sanarwar ta tabbatar da cewa duk wadansu fiyayyen da wasu hukumomin Gwamnatin jihar suka bayar da wani fili ga wani ko wasu ba bisa ka’ida ba duk an soke wadan nan filayen da ake ikirarin an bayar a kan son zuciya.

Sanarwar ta ci gaba da bayanin cewa Gwamnati za ta binciki irin yadda aka yi wannan aikin rabon Filaye ba bisa ka’ida ba, don haka Gwamnatin ta soke irin wannan rabon filayen.

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce gano cewa wadansu jami’an Gwamnati sun sayar da filayen Gwamnati ba bisa ka’ida ba.

“Saboda haka Gwamnatin ta ce daga rana irin ta yau, Gwamnatin ce kawai karkashin ma’aikatar Filaye da Safiyo keda ikon Sayar da duk wani fili mallakar Gwamnatin Jihar”.

About andiya

Check Also

Backward Integration: Dangote Targets 700,000MT of Refined Sugar in Four years

As Q1 revenue rise by 20.1% to N122.7bn   Dangote Sugar Refinery Plc (DSR) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.