Buri Ne Ya Yiwa’Yan Mata Yawa:- Amma Akwai Mazajen Aure – Dakta Mansur Sokot
Akwai mazaje ma ba miji ba, suna can buhu-buhu a gidan kallon bal. Saboda irin burin da mata su ka ci ne ya sa samarin su ka fita harkarsu su ka koma kallon ball tukuru.
Masu mutuwar zuciya daga cikin mazan su ka koma neman auren-jari. Kun ga anyi ‘balance’ ke nan. Don haka kowa sai ya ci wuya. Shi babu mata, ke kuma babu miji saboda kowa ya dauko “dala ba gammo”.
A shekarun baya, mata sun wahalar da maza a fannin soyayya. Sai a samu mace daya tana wasan-kura da samari goma kuma kowa a cikinsu so ya ke ta ce shi ta ke so ya aureta. Ita kuma tana ta wajigasu kamar kwallon ludo.Ita dama duniya rawar ‘yan mata ce, yau kana gaba, gobe sai ka dawo baya. Ba zan manta ba, akwai wacce na sani har lissafa sunayen motocin da ake zuwa wajenta da su wajenta ta ke yi saboda buri da karya. Yadda ta dama, haka samarin suka dinga sha amma a karshe kauye mu ka kaita.Duk irin misalan da su ke a doron kasa ba sa zama izina a wajen matan yanzu. Yawancin masu cewa sun rasa miji dinnan sun samu damar aure su ka yi wasa da ita saboda buri.
Ita dama yar talaka ta shiga uku idan tace buri, ke a suwa kuma? Bayan kin san rayuwa a gidanku. To suma ‘ya’yan masu kudin jikinsu gaya musu yake balle kuma ke. Mai karatu tafi cikin GRA ko Abuja ka sha mamaki, sai ka samu mace ta kai shekara 40 a zaune, ta zama sanata a gidansu.
Allah na tuba, duk sanda mace ta kai 40 a gida kuma ta cigaba da jiran mai kudi ai ta samu matsalar kwakwalwa. Ahirr dinku ‘yan uwana mata, bahaushe yace “Da babu gwara ba dadi” Kuma idan hagu taki sai a koma dama.
Wannan dalilin ne yasa kuke ta bushewa, kullum a rame, cikin tunani da rashin lafiya. Ga kuma uwa da yan uwa sun sako ki gaba da maganganu na neman kai da ke. Saboda kin tare mata hanya, ga kawayenki can sai haihuwa su ke yi, sai dai idan kun hadu su baki raino ki ‘dana rainon jariri. Allah ya aurar da kowa da alheri.
Allahumma amin