Home / Uncategorized / Burin Gwamnan Jihar Zamfara Kawo Ci Gaba Ga Al’Umma –  Dr Suleiman Shinkafi

Burin Gwamnan Jihar Zamfara Kawo Ci Gaba Ga Al’Umma –  Dr Suleiman Shinkafi

IMRANA ABDULLAHI

AN bayyana Gwamnan Jihar Zamfara a matsayin wanda ke aiki dare da rana safiya da maraice domin kawo ci gaban al’ummar Jihar Zamfara, arewacin Najeriya da kasa baki daya.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana hakan a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai inda ya ce, “Babban burin Gwamnan Jihar Zamfara shi ne ganin rayuwar al’umma ta inganta a koda yaushe, don haka muna nan tare da shi ba kuma za mu kauce masa ba a koda yaushe”.

Dokta Shinkafi ya ci gaba da cewa akwai wani gagarumin ci gaban da Gwamnan Jihar Zamfara ya kawo na yin Noman Buhu da mata da yawa za su amfana wanda ake shirin kaddamarwa kwanan nan.

” Gwamna ne ya kawo wannan shirin mu iyakar mu kawai mu aiwatar, mum dauko mutane daga kasar Isra’ila za su zo ranar biyar ga wata azo a ta fi Shinkafi domin koya wa mata dari uku (300) yadda ake wannan Noman na buhu. A wannan Noman na buhu ana iya shuka Tumaturi, Kara’s, Albasa mai Lawashi ( Ganye) da Dankalin Turawa kuma ko inda ba a shuka Dankalin Turawa idan suka zo za su Sanya wa kasar sinadari su tabbatar kasar ta inganta a rika Noman Dankalin Turawa lafiya kalau kuma wannan horaswar da za a yi mata kawai za a yi wa  bayan an samar da horon kowace mace za a ba ta adadin abin da ya dace a ba ta domin a yi mata shukar a kuma hada mata a nuna mata yadda za ta tafiyar da shukar a cikin gidan ta ba sai ta ta fi Gona ba, za ta iya dibar Tumatur, Kubewa, Dankali da albasa komai kuma za ta iya diba duk ta yi miya a cikin gidanta ko ta sayar ko yi wa makwabta kyauta.

Wannan tsarin Noman cikin buhu zai kawo sauki kwarai musamman ta fuskar rashin tsaron da ake fuskanta a yanzu.

” Kowace mazaba za a dauko mace Goma Goma sai a hada su gaba daya a Koyar da su Noman Buhunhuna a kuma tabbatar an yi Noman da yawa sun girbe sun kuma samu amfani.

Za kuma a ba su wani tallafi kadan domin ganin Noman ya ci gaba.

Ya kara da cewa ” bayan hakan kuma yi shawarar cewa za a zo a horas da matasa guda 50 ilimin Na’ura mai kwakwalwa ta yadda za su iya yin zane- zane a kan na’ura mai kwakwalwa kuma kowane matashi idan an Koyar da shi za a bashi na’ura mai kwakwalwa guda daya ya ci gaba da aikin neman abincinsa saboda hakan ne zai taimaka ta fuskar rage wa jama’a talauci, a kuma ci gaba da yi wa Gwamnatin Muhammad Bello Matawalle addu’a.

” Nesanta jama’a da zaman kashe Wando da bunkasar tattalin arzikin jama’a zai kara inganta kwarai, wanda a halin yanzu mata Zawarori da wadanda aka kashe mazajensu ba za su sake yin kuka ba domin muna son yin amfani da wannan tsarin a ko’ina da ake da sansanin yan gudun hijira zamu Koyar da su wannan Noma na Buhu a ba su kasar da za su yi Noman a ba su sinadarin yin Noman da irin shukar baki daya.

A kasar Afrika ta Kudu da dukkan kasashen da suka ci gaba hakan ake yi, Jihohi da dama a Najeriya da aka samu ci gaba hakan dai ake yi, shi yasa muka gayyace su Jihar Zamfara a fara da karamar hukuma Shinkafi.

Dokta Shinkafi ya ci gaba da bayanin cewa Ofishinsa na mai ba Gwanna shawara a kan hulda da kuma samar da yarjeniyoyi da kasashen waje ne karkashin Gwamna Muhammadu Bello Matawalle zai dauki nauyin wannan shirin.

Za kuma mu rubuta wa Gwamna irin nasarorin da aka samu sannan mu nemi mai girma Gwamna ya ba mu damar shiga kowace karamar hukuma domin yin wannan aikin horaswa na Noman Buhu.

A kasar Zimbabwe wannan tsarin Noman buhu ya taimakawa mata suka fita daga talaucin da suke ciki a can baya, har ta kai ga abin ya bunkasa sai da Gwamnati taje gefen gari ta samawa kowace mace yankin wurin da za ta yi Noman buhu na kanta sakamakon irin gasar da ake yi don haka idan Allah ya amince mata za su tserewa tsara da ikon Allah.

“Idan an aiwatar da wannan Noman buhu baki daya tsawon lokacin da zai dauka sati hudu baki daya a sati na biyar sai girbi kawai kuma yayan da ya yi ne ake cirewa a kuma barshi ya ci gaba da yin yaya ya kuma ci gaba har tsawon watanni uku zuwa hudu ana dibar yayan ya dai danganta da yawan Buhunan da mutum mai Noman ya Sanya domin jerasu ake yi.

Kai idan ma baka da buhun sai ka samu kwalbar Lemun kwalba la dasa irin domin iri ne mai inganci da hukumar lafiya ta duniya ta amince da shi cewa ya na amfani sosai ga jikin dan Adam ta wajen kara samun lafiya da kuzari.

Kuma kai idan ma baka da fili har a jikin bangonka zaka iya yin shukar kuma ta yi a kuma samu amfanin da ake bukata na samun amfanin Gona.

A wajen wannan taron za mu nunawa jama’ar da suka halarci taron irin yadda kasashe da wasu Jihohi a nan Najeriya suka ci gaba wajen yin wannan Noman kusan Jihohi shida zuwa Bakwai aka samu nasarar yin wannan Noman buhu don haka mu ne dai na farko da za mu fara har mu kai shi arewacin Najeriya kuma da izinin Allah amfani da tsarin wajen ciyar da matan mu Zawarawa da wadanda aka kashe masu mazaje kowa ya ci gaba.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya ce babban dalilin da ya sa ya dauki aniyar kawo wannan shirin Jihar Zamfara shin tun farko dai mai girma Gwamnan Zamfara mutum ne mai jin shawarar duk masu bashi shawara da ya nada, domin ya taba gaya Mani cewa duk abin da zai ciyar da jama’a gaba talakan Jihar Zamfara ya amfana to lallai ya ba ni izini in yi shi don haka ne da muka hadu da wadannan mutane na ga dacewar in roki mutanen nan suzo Jihar Zamfara domin jama’a su amfana.

Hakan ya sa muka ga ya dace a fara yin Gwajin wannan shirin a karamar hukumar Shinkafi da amincewar mai girma Gwamnan Jihar Zamfara, sai kuma mu ga shin yaya za a yi nan gaba, kasancewar Gwamna na bukatar kowane dan Jihar Zamfara na cikin ni’ima da walwala.

“Kai wannan matsalar tsaron da take faruwa  Jihar Zamfara ta damu Gwamna kwarai har ta na hana shi yin Bacci kullum ya na cikin damuwa don haka duk abin da zai kawo sauki shi ake kokarin yi don haka tun da mun rantse da alkur’ani za mu ci gaba da aiki baki iya karfin mu domin ganin al’umma ta samu ci gaba da nasarori masu masu yawa  kwarai.

“Mun dauki matakai masu karfi masu  zurfi kwarai domin abin da muka yi shi ne zamu fara da mata guda dari uku (300) idan muka yi wannan horaswar a sakatariyar karamar hukumar Shinkafi za a ba su horo na tsawon kwanaki biyar idan an kammala za a ba su satifiket a madadin mai girma Gwamna domin sunan sa ne “Gwamna Matawalle empowerment projects on Sack farming”, wato wani shiri ne na mai girma Gwamna domin Tallafawa mutane su dogara da kansu, wanda bayan an ba su sai kuma a ba su buhu hunan da kuma irin shukar da za a ba su. Kuma tuni har an yi masu shukar suna nan ana ranonsu daga nan kuma sai a dauka a ba kowa nasa sai kuma mu ci gaba da bibiya har a kai ga abin da za a yi a nan gaba musamman ta fuskar kulawa da ita shukar.

Kuma abin da nake son jama’a su gane shi ne Malaman Gona ne daga kasar Isra’ila za su yi wannan karantarwar, akwai ma Jihar Bayelsa mutane suka tura har kasar Isra’ila domin su ga yadda ake wannan Noman Buhu, kamar yadda aka Sani a kasar Bayarlsa ba wata kasar yin Noma ta kwarai amma da wannan tsarin na Noman Buhun nan suke cin abinci su yi miya su kai kuma kasuwa jama’a na saye a hannunsu, muma bukatar mu kenan mata na cikin gidajensu ba sai sun je Gonaki ba kafin Allah ya dauke mana wannan abu ba domin nan ba da dadewa ba Gwamna ya dauki matakai na ganin lamarin ya kawo karshe da ikon Allah.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya yi kira ga jama’ar Jihar Zamfara da su ci gaba da bayar da duk wani cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwamna Muhammad Bello Matawalle cikakkrn hadin kai da goyon baya matsayinsa na Gwamna mai tausayi, jin kan jama’a da damuwa da halin da ake ciki a koda yaushe domin ba a ta ba yin Gwamna mai tausayin jama’a ba kamar shi. Muna kuma shaidawa jama’a cewa a ci gaba da bayar da hadin kai ga Gwamna Matawalle domin ya na da tsare tsare kwarai da zai aiwatarwa domin ci gaban al’umma kowa ya yi farin ciki, Yan kasuwa ana nan ana yi masu shiri yadda za su yi dariyar farin ciki haka kuma yan makaranta, ma’aikatan Gwamnati duk ana yi masu shiri mai kyau.

“Su Sani fa abin da Gwamna ya ce jama’a su kare kansu wannan fa gaskiya ne domin ba wani zabi sai hakan don hakan ya dace kowa ya Sani a Jihar Zamfara akwai mutane masu kishin jama’arsu wanda hakan ya sa Sanata Hassan Nasiha ya ajiye ya dawo Jihar Zamfara ya zama mataimakin Gwamna ya kuma dauko Sakataren Gwamnati da shugaban ma’aikata duk da suka dace aka Sanya su domin su tallafa kamar masu ba Gwamna shawara, kwamishinoni da daukacin mukartaban Gwamnati baki daya duk su na jajircewa a koda yaushe wajen ganin an samu ci gaba.

About andiya

Check Also

Remain steadfast against security challenges” – CDS General Musa to army officers and men

  The Chief of Defence Staff , General Christopher Musa has tasked the Nigeria Army …

Leave a Reply

Your email address will not be published.