Home / MUKALA / Dattawan Arewa Sun Yaba Wa Gwamna Bello Matawalle Bisa Fadakar Da Jama’a Su Kare Kansu

Dattawan Arewa Sun Yaba Wa Gwamna Bello Matawalle Bisa Fadakar Da Jama’a Su Kare Kansu

IMRANA ABDULLAHI
…Hakika mutanen yankin Arewa maso Yamma Sun Wahala kwarai da ayyukan yan bindiga
Kungiyar tabbatar da ci gaban  Arewa domin samar da zaman lafiya da adalci, mai suna “Arewa Development Forum For Peace And Justice” sun tabbatar da bayar da cikakken hadin kai da goyon bayansu ga Gwamna Muhammadu Bello Matawalle bisa irin yadda ya fadakar da al’ummar Jihar kan kowa ya tashi ya kare kansa daga matsalar yan bindiga.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a bayanin bayan taron da suka yi a Kaduna, inda suka yanke hukuncin goyon bayan Gwamnan da ya bayar da umarni ga jama’a kowa ya tashi ya kare kansa daga duk wani batagarin dan bindigar da ke cikin al’umma.
A cikin wata takardar da ke dauke da da hannun Alhaji Zubairu A Mustafa da aka rabawa manema labarai a Kaduna sun jinjinawa Gwamna Muhammadu Bello Matawalle bisa wannan matakin da ya dauka.
Yayan kungiyar a cikin takardar da suka raba wa manema labarai sun yi kira ga daukacin sauran Gwamnonin yankin da su hada kansu su kuma samar da wata rundunar jami’an sa kai da za su yi aikin hadin Gwiwa dom8n yakar matsalar yan bindiga masu satar mutane da kuma sayar Shanu da lalata dukiyar al’umma a wurare daban daban, musamman sun bayar da misali da irin rundunar da Gwamnan Zamfara ya kaddamar ta al’umma su kare kansu a ranar Asabar da ta gabata.
Kungiyar sun kuma yi Allah wadai da irin yadda shugaban rundunar sojan Najeriya Janar Lucky Irabo ya yi saurin yin suka ga wannan kokari na Gwamnan Jihar Zamfara tare ma da wadansu yan Boko da ba su da wata masaniyar abin da ke faruwa na satar mutane, kashe karshe da sauran hare haren da ake yi a cikin yankin Arewa maso Yammacin Najeriya wanda kuma yan bindigar da ake zargi ke aikatawa.
Yan kwanakin da suka gabata, yan Ta’adda sun kai hari ga wata mahakar ma’adinai a garin Shuroro na Jihar Neja da suka kashe a kalla jami’an tsaro Goma Sha Bakwai 17 da duka hada da sojoji, Yan Sanda da kuma jami’an sa kai suka kuma sace mutanen kasar Cina hudu. Duk wannan na zuwa ne yan kwanaki bayan samun rahotannin zargin kai hari tare da satar mutane da yawa a wasu kauyuka na jihohin Kaduna, Kebbi, Neja, Katsina, Zamfara da Sakkwato da babu wani abin da aka yi.
Wannan mugun aikin da ake aiwatarwa ga yan Najeriya da garuruwansu kawai ya na ta ci gaba da gudana ba tare da daukar wani mataki ba, amma duk da hakan sai kawai ake ta kokarin wanke kwakwalwar jama’a daga wasu manyan jami’an tsaro da kuma wadanda ke ganin sun yi karatu da ba su goyon bayan al’umma su dauki makami domin su kare kansu.
Mu a gare mu, wadannan mutane masu kai hare haren su na kokarin haifar da nakasu ne ga shiri da duk wani tsarin Gwamnati haka kuma masu kokarin fitowa fili su na yin suka ga wannan tsarin na Gwamna Mutawalle duk su na kokarin kawo nakasu ne ga tsarin samar da ingantacce kuma sahihin zaman lafiyar jama’a domin yan bindigar da suke kai hare hare haka kawai su na haifar da matsala ne kawai da lalata dukiyar jama’a tare da garuruwansu da duk abin da mutane suka mallaka na rayuwa.
A ranar Alhamis, ranar 30 ga watan Yuni, a wajen Jana’izar da aka yi bayan kashe wani Malamin addinin kirista a Kaduna, babban Malamin addinin Kirista a Kaduna Rabaran Mathew Man – Oso Ndagoso ya fito fili ya goyi bayan matakin da Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya dauka na jama’a su mallaki makamai ta hanyar doka domin kare kansu daga garin yan bindiga.
Akwai wani kimanin addinin Kirista da ya bayar da misali da Gwamna Aminu Bello Masari na Jihar Katsina da tun farko shi ne ya fara yin cikakken bayani a game da hakan da ya ce zai taimakawa ayyukan jami’an tsaro wajen yaki da yan Ta’adda a yankin.
Ga duk wadanda ke cewa hakan ba dai dai ba ne wai hakan zai iya zama wani abu daban a cikin al’umma to, wake goyon baya da kuma bayar da izini ga yan bindigar da ke daukar makamai suna kashe jama’a su na Sace masu dukiya da suke yin amfani da AK 47 da sauran miyagun makamai daban daban a wannan yankin namu?
Ya zama dole shugabannin mu su tashi tsaye tun yanzu domin daukar matakin da ya dace in kuma ba haka ba za mu kasance wadanda za a rika halakarwa haka kawai ba gaira ba dalili saboda yan kalilan din mutane za su rika daukar makami su rika afkawa mutanen da suka fi yawa.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa idan har Gwamnati ta kasa daukar wani mataki a yanzu, ya dace su Sani cewa idan tura ta kai Bango kowa zai nemi mafita ne da ta dace da shi domin samun mafita wanda kuma shi ne daukar makamai, saboda Gwamnati ba za ta iya kare su ba daga yan ina da kisa tare da Kone masu garuruwa.
Mutane da yawa a yankin Jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina da Sakkwato da lamarin yan bindigar nan ya shafe su duk sun yi na’am da wannan matakin domin zai taimaka a samu warware wannan matsalar ta yan bindiga da suke kashe al’umma haka kawai dare da rana ba gaira ba dalili.
Idan aka yi duba da irin mutanen yankin Kudu maso Yamma suka yi kokarin dakile aikin yan Ta’adda da ake zargin masu kiwon Dabbobi ne da aka dakile su da akalla yawan kashi 75 cikin dari da ake ganin kungiyar AMOTEKUN ta aiwatar da hadin Gwiwar jami’an tsaron da kai na cikin al’umma wannan a bayya ne yake ga kowa.
Daga Zurmi zuwa Tsafe zuwa Bakura har Maradun zuwa Shinkafi wadannan yan bindigan sun ci gaba da aiwatar da mugun aikinsu na kaiwa jama’ar da ba su ji ba ba su gani ba hari domin kawai su jami’an tsaron da ke aiki ba su da yawa, ba su kuma da wadatattun kayan aiki da za su iya yin maganin matsalar yan bindigar da ke zubar da jinin jama’a haka kawai Dare da Rana Safe da Yamma.
A wannan yanayin Gwamna Matawalle ne ya san inda yake yi wa jama’a ciwo, don haka muke kira ga daukacin jama’a su kara bashi cikakken hadin kai da goyon baya kuma mu na yin kira ga mutanen karkara da su tabbatar da mallakar makamai ta hanyar da doka ta tsara domin kare kawunansu daga matsalar yan bindiga da ayyukansu.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa hakika suna goyon bayan duk wani shugaban da zai tashe tsaye wajen tabbatar da ganin ya dauki matakan da suka dace bisa tsarin dokar kasa da nufin samar da zaman lafiya da tsaron lafiya da dukiyar al’umma baki daya.
Babu wani abu mai muhimmanci da ya wuce a samu shugaba ya na kokarin taka rawar da ya dace ya taka domin kare lafiya da dukiyar al’umma a madadin kawai a koda yaushe ya rika halartar Sallar Jana’izar wadanda aka kashe da kuma zuwa gaisuwar mutuwarsu bayan an kai masu hare hare.
Daukar wadansu matakai da suka hada da taimakawa sojoji da yan Sanda, samar da kayan aiki da kuma bayar da dama ga al’umma su kare kansu duk abubuwa ne masu muhimmanci kwarai wanda hakan shi ne mafita da za ta samar da zaman lafiya da karuwar arzikin jama’a musamman a wannan lokacin da ake matukar bukatar samun tsaron lafiya da dukiyar jama’a baki daya.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.