Home / Labarai / BURIN MU TAIMAKAWA MARAYU DA MARASA GALIHU – USMAN ZAKARIYYA

BURIN MU TAIMAKAWA MARAYU DA MARASA GALIHU – USMAN ZAKARIYYA

IMRANA ABDULLAHI
Sanata Uba Sani, mai wakiltar yankin Kaduna ta tsakiya, ya yi kira ga daukacin al’umma da su mayar da hankali wajen taimakawa marayu da marasa galihu da ke cikin jama’a ta yadda al’amura za su ci gaba da inganta.
Sanata Uba Sani, ya bayyana hakan ne a wajen babban taron yaye daliban makarantar Atiku Auwal Madarasatul Islamiyya, da ke kan titin Lome cikin unguwar Rimi a Kaduna, tarayyar Najeriya.
Sanata Uba Sani, wanda ya samu wakilcin Usman Zakariyya, ya ce abu ne mai matukar alfanu ga dukkan daukacin al’umma su rika taimakawa harkokin addinin Islama wanda hakan zai taimaka wajen ci gaban al’umma.
Alhaji Usman Zakariyya, dan siyasa ne da ke takarar neman zama dan majalisar dokokin Jihar Kaduna a mazabar Doka/ Gabasawa, ya bayyana cewa ya fito neman wannan kujerar ne domin taimakawa al’amuran addini da dukkan harkokin ci gaban jama’a baki daya.
Zakariyya ya kuma bayar da taimako ga makarantar na kashin kansa na kudi naira dubu Hamsin (50,000)
Ya ci gaba da cewa wani dalilin kuma da ya sa shi fitowa takarar shi ne domin inganta rayuwar matasa da kuma fadakar da matasan su san abin da ya dace da su a wajen harkokin siyasa ta yadda za su fito domin a dama da su a tsarin.

About andiya

Check Also

Gwamna Radda Ya Koka Da Cewa  22 LGAs Marasa lafiya A Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Dakta Dikko Umar Radda ya koka kan matsalar tsaro a jihar Katsina, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.