Home / Kasuwanci / CIRE TALLAFIN MAI; A NEMAWA JAMA’A SAUKIN RAYUWA – AMINU IBRAHIM

CIRE TALLAFIN MAI; A NEMAWA JAMA’A SAUKIN RAYUWA – AMINU IBRAHIM

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

Aminu Ibrahim shugaba ne na A S Goronyo a bangaren Keke – Napep, ya bayyana batun tallafin Man fetur da cewa a halin yanzu kowa ya ga al’amari ne mai muhimmanci da taimakon kowa don haka a samo hanyoyin da jama’a za su samu sauki a kasa.

Aminu Ibrahim ya bayyana hakan ne a lokacin wata zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke Kaduna.

“Hakika ana ganin cewa tsohuwar Gwamnati ce ba ta Sanya batun tallafin ba a cikin tsarin kasafin kudi ba, to Gwamnatin yanzu kuma ana ganin shugaban kasa na yin aiki tukuru yana kai wa da dawowa domin ganin an samu dai- daituwar al’amura don haka muke fata a samu nasara a kan wannan tsananin rayuwa da jama’a ke ciki, don haka Allah ya kawo mana mafita”.

A game da batun farashin mai da ke cizon jama’a sakamakon cire tallafin mai kuwa, sai ya ce hakika dukkan mutumin da ke harkar sufuri idan bai yi a hankali ba to, zai rika batawa da jama’a ne kawai, saboda yanayin farashin man yasa wasu mutane da yawa ba su iya biyan kudin ababen hawan da suke hawa na yan kasuwa. Su kuma direbobin ababen hawan Mai ya yi masu tsada har ta kai ga akwai wadansu direbobin da ba za su iya biyan kudin balas ba, wanda sakamakon hakan a yanzu direbobi kalilan ne kawai ke iya sama wa masu ababen hawan balas din kudin da aka yi ka’ida da su na abin hawa tun daga Motoci zuwa Baburan hawa.

” Akwai wani mutum da ya tabbatar Mani cewa ya sha man naira dubu biyar amma abin da ya samu a sama bayan ya zagaya duk ya yi yawon haya dari biyu kawai ya samu bayan ya samu kudin man da yasha dubu biyar, saboda haka abin ya zama bauta kenan kawai tun da ga direba da iyali kuma ana cikin tsanani ba biyan bukata domin kowa na cikin takura da damuwa sakamakon yanayin da ake ciki.

A saboda haka ne muke yin kira ga Gwamnati da ta samawa al’umma sauki domin wannan tallafin mai da ake magana a can baya koda dai wasu na ci da gumin wasu amma sauki na zuwa ga al’umma koda yake dai sun ce zuwa gaba kadan wai talaka zai ji dadi muna addu’ar samun hakan.

“Mu babbar bukatar mu ita ce ayi wa jama’a adalci ayi masu aikin da za su fita cikin halin yau da suke ciki. Su kuma jama’a su yi wa Gwamnati adalci, saboda idan mun koma yin zage – zage da batanci ga shugabanni lamarin ba zai taimaka ba domin yin abin da zai kawo mafita ne adalci kawai a samu sauki kuma har Allah ya taimake mu.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.