Home / Big News / COVID-19: An Bayyana Dokar Hana Fita A Kaduna  

COVID-19: An Bayyana Dokar Hana Fita A Kaduna  

 Imrana Abdullahi
Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad ta bayyana kafa dokar hana fita a daukacin Jihar baki daya, saboda matsalar da aka samu ta rashin bin matakan da aka dauka tun farko domin hana samuwar cutar Covid- 19 da ake kira Korona bairus.
Sai dai Gwamnatin ta ware wata hanya guda daya da matafiya za su rika amfani da ita wato wadanda suka fito daga wadansu Jihohi za su bi ta kaduna su wuce an ware masu hanyar da ke cikin garin kaduna ta Yamma.
The Deputy Governor, Dr Hadiza Balarabe  who made this known on Thursday, in  the second state broadcast in two days,  said that the decision is in line with the 1999 constitution.
Kamar yadda aka bayyana cewa ” kamar yadda doka ta bani dama wato a matsayina na Gwamna kamar yadda yake kunshe a cikin kundin tsarin mulkin Nijeriya Nijeriya shekarar 1999,  sashe na 2 da na 8 domin killacewa doka 1926 da kuma dokar lafiya ta Jihar kaduna 1917″.
Dakta Balarabe ta tabbatar da cewa hakika wannan dokar ta hana fita an Sanya ta ne domin cuta mai yaduwa ta Covid 19 da ake kira da Korona bairus, hakika tana yaduwa a tsakanin jama’a daga mutum zuwa wani mutum.
Don haka ne kwamitin da aka kafa a Jihar kaduna domin duba yadda wannan yanayi ya zauna ya kuma duba dukkan yadda ake bin wannan dokar da aka Sanya tun farko a kan Korona bairus.
Wannan kwamitin ya duba da kyau irin yadda ba a bin wannan doka da matakan da aka dauka a kan lamarin cutar Korona inda Gwamnatin ke ta shelanta batun da jan hankalin jama’a ta hanyar yin cikakkun bayanai amma irin yadda aka dauki lamarin yasa dole Gwamanti ta dauki mataki na gaba.
Sai dai kamar yadda Samuel Aruwan kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida ya shaidawa manema labarai cewa akwai tsarin taimakawa marasa galihu a wannan yanayi.
Mataimakiyar Gwamnan ta kuma yi gargadi da kakkausar Murya cewa a yau Alhamis, 26, ha watan Maris 2020, dukkan mutanen Jihar kaduna dole su zauna a gida.babu batun aiki, kasuwanci ko kuma ayyukan Ibada duk ba a amince da ko daya da aka ami ce da su.
Mataimakiyar Gwamnan ta bayyana cewa da akwai wadansu mutanen da suke gudanar da muhimman ayyukan ci gaban kasa da za su iya gudanar da ayyukansu kamar jami’an kiwon lafiya, jami’an kashe Gobara, jami’an tsaro”
Dakta Balarabe ta kuma bayar da tabbacin cewa za a yi amfani da jami’an tsaro domin tabbatar da cewa mutane sun kiyaye dokar “tuni aka ba su umarnin kamawa da hukuma dukkan wani da ya karya wannan doka
Kuma Gwamnatin jihar kaduna ta bayyana cewa babu wani masallaci ko coci da za a yi sallar Juma’a da Ibadar Kiristoci a kusa da wurin bautar ko kuma wani wuri na daban
Mataimakiyar Gwamnan ta bayyana farin ciki ga dukkan wadanda za su taimakawa al’umma da bayanai game da wanda ake zargi da Covid 19 a cikin jama’a ko kuma wadanda suke kin bin ka domin da aka Sanya.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.