Home / Big News / Cutar Korona :Masari Ya Rufe Fadar Sarkin Daura

Cutar Korona :Masari Ya Rufe Fadar Sarkin Daura

Sakamakon Matsalar kamuwar da mutane ke yi da cutar Covid- 19 da ake kira Korona yasa Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bayar da umarnin rufe fadar mai martaba Sarkin Daura.
Aminu Masari ya bayyana wa manema labarai a Katsina cewa an dauki samfurin Jinin mutane sama da Tamanin da aka ta fi da shi Abuja domin yin Gwaji.
Masari ya kuma ce an dauki samfurin jinin me daga mutanen da suke fadar da zagayen fadar domin a tantance lafiyarsu, wanda idan an same su da cutar za a dauki matakin kulawa da su.
Kuma an bayyana cewa an killace dimbin wadansu mutane saboda matsalar cutar Korona.

About andiya

Check Also

Governor Tambuwal To ASUU;  Resume Classes or Forfeit Your Salary Fore With

…Reads Riot Act To ASUU Sokoto Varsity Sokoto state government has spent the sum of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.