Home / Labarai / Da dumi duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Wanke Dauda Lawal Dare A Matsayin Dantakarar Gwamnan Zamfara

Da dumi duminsa: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Wanke Dauda Lawal Dare A Matsayin Dantakarar Gwamnan Zamfara

 

IMRANA ABDULLAHI (NORTHERN NIGERIA)

 

 

Kotun daukaka kara da ke shiyyar Sakkwato a arewacin tarayyar Najeriya ta tabbatar da dan takarar Gwamnan Jihar Zamfara Dauda Lawal Dare a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP, a zabe mai zuwa na shekarar 2023 da za a yi a watan Fabrairu mai zuwa.

 

 

Alkalin kotun a halin yanzu ya jingine hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Gusau ta yi inda ta hana Dauda Lawal Dare tsayawa takarar Gwamnan.

 

Idan dai za a iya tunawa Injiniya Ibrahim Shehu daya daga cikin yan takarar Gwamnan ne ya kai karar Dauda Lawal bisa abin da ya kira an yi ba dai dai ba a wajen zaben fitar da dan takarar Gwamnan Jihar Zamfara a Jam’iyyar PDP.

About andiya

Check Also

Aliyu Sokoto tasks cabinet on transformation drive, ‘ be committed and sincere 

  By Suleiman Adamu, Sokoto SOKOTO state Governor Dr Ahmed Aliyu Sokoto has tasked members …

Leave a Reply

Your email address will not be published.