Home / News / ZAMU BA TINUBU, SHATIMA KURI’A MILIYAN 12 – INJINIYA KAILANI 

ZAMU BA TINUBU, SHATIMA KURI’A MILIYAN 12 – INJINIYA KAILANI 

 

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Shugaban kungiyar a kasa a tsare a raka dukkan kuri’un da jama’a suka kada a kasa baki daya Iniiniya Dokta Kailani Muhammad ya bayar da tabbacin cewa za su bayar da kuri’u miliyan Goma sha biyu a zabe mai zuwa ga Tinubu da Kashim Shatima.
Injiniya Kailani Muhammad ya bayyana cewa kamar yadda suka bayar a matakin kungiyar na kasa za su tabbatar sun yi irin yadda suka gudanar da aikin samun nasara da shugaba Muhammadu Buhari ya samu ta fuskar bashi dimbin kuri’a wanda sakamakon hakan ya lashe zabe da gagarumin rinjaye.
Injiniya Kailani Muhammad ya bayyana hakan ne a wajen wani babban taron Kodinetocin kungiyar da aka yi a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
Kailani ya ci gaba da cewa yayan kungiyar a shirye suke domin yin aikin samar da kuri’a ga Asiwaju Bola Ahmad Tonubu da Sanata Kashim Shatima a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Wannan aikin na kokarin samar da miliyoyin kuri’u ba sabon abu bane ga yayan wannan kungiya don haka zamu aiwatar da shi ba tare da gajiyawa ba ko kadan”, inji Kailani Muhammad.

About andiya

Check Also

Sanata Barau Jibrin  Ya Jajantawa Iyalan Wadanda Aka Kashe A Tudun Biri, Ya Bukaci A Gudanar Da Bincike

Daga Imrana Abdullahi Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau  Jibrin, ya jajantawa iyalan wadanda harin …

Leave a Reply

Your email address will not be published.