Home / Labarai / Dalilin Da Yasa Na Gabatar Da Kudirin Masu Aikatau – Sanata Babangida Hussaini

Dalilin Da Yasa Na Gabatar Da Kudirin Masu Aikatau – Sanata Babangida Hussaini

 

Daga Bashir Bello, Majalisa Abuja.

Sanata Babangida Hussaini, shugaban kwamitin gyaran hanyoyin Gwamnatin tarayya a majalisar Dattawa ta kasa ya bayyana dalilan da suka Sanya ya gabatar da kudirin masu Aikatau a gidajen jama’a a gaban majalisar domin daukar mataki.

Sanata Babangida Hussaini ya bayyana hakan ne jim kadan bayan da ya gabatar da kudirin a gaban majalisa, inda ya ce shi wannan kudirin ya hada ne da masu yin gadi, da sauran aikace aikace a gidajen jama’a da suka shiga cikin rayuwar iyalan jama’a, an kuma gabatar ne domin a samar da kariya da kulawar da ta kamata domin hakki ne ga wanda ya dauke su aiki ya tsare mutuncinsu ya ba su hakkin da ya kamata ya ba su kariya ya kuma ba su Albashi wanda ya kamata ya kare lafiyarsu ya kare mutuncinsu ya kuma tabbatar da cewa ba a yi abin da za a wulakanta su ba .

Sanata Babangida ya ce “kamar yadda muka Sani kamar yadda kowa ya Sani amma a halin yanzu ba haka take faruwa ba, wannan wani bangare kenan na wannan kudirin”

Sai kuma banfare na biyu da batun yake son ya kalla shi ne na shi wanda yake daukar ma’aikata a matsayin ma’aikata na gida, lamarin shi ne ana samun korafe korafe hakika akwai matsaloli da dama da wadansu ma ba su fitowa fili, kuma har ma ana samun wadanda su ake hada baki da su suna bayar da sirrin masu gidajensu ko wani abin da duka ake ko dai wani halin da suke ciki da ake yin amfani da hakan ana cutar da su don haka ne ma daya daga cikin abin da na kawo wanda ya faru kuma bai yi wa kowa dadi a kasar nan ba , a shekara ta 1998 akwai wani babban jami’ar tukin Jirgin sama da ta kasance ita ce mai tukin Jirgin sama ta farko a kamfanin jiragen sama na Najeriya ta na da shekaru 39 a duniya ya rage mata yan watanni ta zama cikakkiyar mai tukin Jirgin sama, amma sai ga shi an hada baki da masu gadinta aka kashe ta kuma bayan sun kashe ta sai har yau maganar da nake yi ba a san ko su waye ba kuma ba a san daga inda suke ba kuma wannan duk kowa ya Sani, sannan kuma ya yanar Gizo ma akwai wanda kwanaki aka yi wanda wata yarinyar gida ce aka ba ta jariri ta kula da shi amma ta rika yin tsalle ta na taka shi, to, wannan fa wadanda ma muka gani kenan kawai.

Kuma ko a kwanan nan sai da ministar mata ta kasa sai da ta samu yan Sanda da kanta ta ce masu aje Jihar Anambara a nemi wata domin ta Sanya reza ta tsagawa yarinyar gidanta baya wato ta tsatstsaga mata baya, balantana kuma wadanda ake batawa a matsayinsu na mata domin kawai abubuwa ne da babu tsari ba doka a ciki kungiyar kwadago ta yi doka domin tsaro da kariya na rukunin wadannan ma’aikata daukar ma’aikatan da hakkinsu, na wata ma’aikata da ke kula da wannan domin a tabbatar kowane ma’aikaci an bashi hakkinsa saboda haka ni kudirin da na kawo shi ne ayi wannan tsarin a tabbatar da cewa kowa an bashi hakkinsa da niyyar a kafa ko ma’aikata ko wata hukuma ko dai wani abu kwakkwara a ma’aikatar aiki da kwadago a tabbatar da cewa an kula da hakkin masu yin irin wannan aikin a gidajen jama’a.

Misali “ko a kasar Saudiyya dukkan mu mun san masu zuwa Aikatau wani ke samar masu aikin kuma ana biyansu a misali ka ce kana neman ka dauki direba akwai kuma hukumomin daukar ma’aikata da ke da alhakin daukar ma’aikatan da kuma tace su da tarihin Fasalin jikinsu (bi metric) da ko me ya faru wannan mutumin ba zai ba ta ba wadannan suna da rajista da ita kanta ma’aikatar kwadago, ka dauki misali yan Aikatau din nan ba zaka rasa shi da direba ba ko mai mashi wanki ko dai saboda yanayin yadda rayuwarmu take ana ta kwaranniya kuma dai harkar gida sai an yi hakan, don haka idan dai zaka ajiye wanda zai yi maka wannan ya san sirrin gidanka da ayyukan gidanka ya dace lallai kana da cikakken bayani da sani a kan wannan mutum domin hakan zai baka kariya. Kuma wanda zai yi maka aikin sai ka tabbatar da ka kare mutuncinsa ka bashi aikin da ya dace baka kuma bashi aikin da zai wulakanta shi ba ka tabbatar wurin kwanansa,nruwa da tsafta duk akwai ka gyara wannan ya dace ace tsari ne na fiye da shekaru Ashirin ma muna da shi wannan shi ne bayani a dunkule a kan kudirin da na gabatar.

A game da yawan lokacin da zai dauka a kammala aiki a kan wannan kudirin kuwa sai Sanata Babangida Hussaini, ya kada baki ya ce tun da dai an mika wa kwamiti wannan batu majalisa kuma ta bayar da tsawon sati hudu don haka ina sarai za a kawo rahoto a sati hudun.

Hakazalika a kan ko akwai tanaje tanaje na doka a kan cin zarafin da aka yi sai ya ce daman fa duk abin da ake yi za a je wajen batun jin ra’ayin jama’a kuma a wajen wannan zaman za mu nemi gudunmawar kungiyoyin kare hakkin bil’adama da ita kanta ma’aikatar da al’umma baki daya hukuncin da yakamata a yi wa wanda ya karya wannan dokar ko daga bangaren masu yin aiki wato yan Aikatau din ko daga bangaren wadanda suke bayar da aikin ko daukar su aikin don haka kowane akwai hukunci wanda dokar za ta yi aikin a kansa idan ya karya wannan dokar

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.