Daga Imrana Abdullahi
Honarabul Saminu Hashim da ake yi wa lakabi da Dan Alhaji, ya bayyana cewa ya fita daga cikin jam’iyyar ADC ne zuwa PDP domin ya samu cikakken sukunin taimakawa al’umma ta yadda za a cimma gaci tare da samun nasarar da kowa ke bukata.
Saminu Hashim Dan Alhaji ya bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna.
Inda ya ci gaba da bayanin cewa duk wanda ya san jam’iyyar ADC musamman a karamar hukumar Kaduna ta Kudu lallai ba da alfahari ba ya santa ne ta dalilinsa.
” A cikin jam’iyyar ADC na yi takarar Kansila kuma na samu nasara amma saboda halin karfakarfa aka kwace kujerar,amma duk da hakan saboda muna yin wannan hidimar siyasa ne domin jama’a ba don kanmu ko aljihinmu ba muke ci gaba da kokarin da muke yi domin Ni ba domin aljihina nake yi ba, inji Dan Alhaji.
Ya kuma kara da ci gaba da yin kalubalen cewa, ” in kuma da wanda ya taba daukar Naira daya ya ba shi to, kuma ita wannan jam’iyyar ta ADC mu muka rike ta da dukiyar mu kuma ba wani amfanin da ya taba zuwa gare mu daga matakin jam’iyyar na kasa. Idan har Kwankwaso da ya gina jam’iyyar NNPP zai koma wata jam’iyya ta ADC to, ina ga mu kuma saboda haka a yanzu lamarin siyasar duk ya canza salo fa dan wancan jam’iyyar zai iya komawa wannan jam’iyyar duk ba abin mamaki ba ne.
“Kamar irin su Nasiru Haruna ya canza daga APC zuwa ADC amma kuma Alhaji Sule Lamido ma ya ce ya na Nan a cikin PDP amma zai iya bayar da gudunmawar a inda ya kamata a ADC, kuma kamar irin su Sanata Makarfi ya na Nan a cikin PDP domin ta akida suke yi duk da wasu na cewa PDP ta mutu.
Sai dan Alhaji ya kara jaddada cewa ba jam’iyya mai adalci irin ta PDP kasancewar nan ne kawai zaka taka rawar ka har a gani a yaba maka, saboda haka ne muke yin kira ga jama’a da kowa ya kwantar da hankalinsa mu koma wannan jam’iyya ne domin a taimakesu.
“Ai takarar kujerar maganar Unguwar Sanusi kamar ma mun yi ta ne da yardar Allah, da ta haɗa da Sabon Gari ta Kudu da Arewa sai Badikko da Kurmin Mashi kamar ma mun lashe ta ne
Sai kuma abin da nake don kowa ya mayar da hankalinsa a kai shi ne duk jam’iyyar da ba za ta baka tikitin tsayawa takara ba dole ne ka nema wa kanka mafita,mutane na matukar nuna soyayyar su a gare mu amma idan ba a ba mu takara ba ta yaya soyayyar su za ta yi amfani.
Yakamata, “mu sa hankalin mu a duk mazabar Badikko wane dan takara ne ya ya ba hawa a kan takardar zabe da ake jefa kuri’a da ita ya yi takarar memba,don haka wannan ne makasudin fita daga wancan jam’iyya zuwa PDP da muke yin kira ga jama’a da su bayar da cikakken hadin kai da goyon bayansu ga jam’iyyar PDP ayi mata ruwan kuri’a idan lokacin zabe ya yi.
THESHIELD Garkuwa