Home / Big News / Jami’an DSS Sun Wuce Da Nasiru El- Rufa’i

Jami’an DSS Sun Wuce Da Nasiru El- Rufa’i

 

A ranar Talatar nan ne jami’an tsaron farin kaya na DSS suka wuce da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i bayan babbar kotun gwamnatin tarayya ta kammala sauraron batun maganar neman hukumar ICPC da ta kai shi kotun na neman a bayar da shi beli.
Ita dai Kotun tarayyar mai zamanta a Kaduna ta sanya ranar 14 ga watan Afrilu ta zama ranar da za a yanke hukunci a game da batun maganar konza a bayar da shi Belin.
Kamar dai yadda lauya mai tsayawa Malam Nasiru Adewole Iyamu,ya ce tawagar nauyin da yake jagoranta na saran za su samu biyan buƙatar da suke neman tun da dai komai tuni aka riga ya aka mikawa kotun baki daya.
Hukumar ICPC dai ta kai karar Malam Nasiru ne bisa tuhume tuhume har guda 10 kuma Malam Nasiru na hannunta tun ranar 19 ga watan A
Fabrairu, in Banda Dan sakinsa da aka yi a ranar 28 ga watan Maris sakamakon mutuwar mahaifiyarsa da ta rasu a Kairo kasar Egypt.
Kamar dai yadda Lauya Iyamu ya ce ana saran tsohon Gwamnan zai halarci wani zaman kotun a ranar 10 ga watan Afrilu,a wata karar da hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta shigar.

An dai tsaurara tsaro a harabar kotun tarayya da ke unguwar NDA cikin garin Kaduna, sai dai an hana manema labarai shiga cikin dakin kotun, an kuma kashe hannu guda na titin da ke zuwa daga babbar  Kasuwar Kaduna zuwa Kawo kasancewar titin na kusa da Kotun ne abin da ya haifar ga gagarumin jerin gwanon motocin hawa da babura ya kuma takura wa masu tafiya a kasa har sai da aka kammala zaman kotun inda Jami’an DSS suka wuce da Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i.

A halin yanzu dai jama’a na jiran yadda za ta kaya a game da batun bayar da Malam Nasiru Bello a ranar 14 ga watan Afrilu.

About andiya

Check Also

Dangote Refinery Recalls Redeployed Engineers

    Dangote Petroleum Refinery has approved the recall of engineers previously redeployed across its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.