Home / Labarai / Dalilin Rushe Gidan Rediyon Vision Mai Gajeren Zango Na Kaduna – Mahadi Shehu

Dalilin Rushe Gidan Rediyon Vision Mai Gajeren Zango Na Kaduna – Mahadi Shehu

Mustapha Imrana Abdullahi
Kamar dai yadda dimbin jama’a ke ta mamakin irin yadda kyakkyawar dangantaka da ke tsakanin Dokta Mahadi Shehu da kuma shugaban kamfanin “Vision Media Service” Alhaji Umar Faruq Musa wanda suka kasance masu kyakkyawar alaka mai kyau da mutunta Juna wanda har Umar Faruq Musa ya kawo wa Dokta Mahadi Shehu kukan halin da yake ciki na kada lasisinsa da hukumar NBC mai kula da bayar da lasisi da kuma kula da ayyukan gidajen rediyo da Talbijin suke gudanar da ayyukansu suke yi masa barazanar rasa lasisin da suka bashi domin kafa rediyo a Kaduna.
Wanda bisa wannan koken da ya kai wa bakinsa dan kasuwa kuma da Allah ya yi dimbin suturar abin duniya Dokta Mahadi Shehu ya dauki abokin nasa Umar Faruq Musa ya kai shi gidansa da ke layin farko 1, 1TPO 486 unguwar Dosa cikin garin Kaduna ya ce masa ya yi gidan rediyo ba tare da ya biya shi kudin haya ba, amma sai ga shi a yanzu an gansu a rana sakamakon tsamin da dangantakarsu ta yi
.
“A wani lokaci can baya Umar Faruq ya kira ne da ya ji an tattauna da ni a gidan rediyon freedom ya ce yaya zaka je kana da gidan rediyo amma sai kaje wajen abokan gamayyar mu, ni kuma na gaya masa ba na zuwa inda ba a gayyace ni ba, bayan da aka tattauna da ni a gidan rediyon Vision a Kaduna sai ya ce sai na biya naira dubu dari, har sai da ya umarci ma’aikatan Vision na Kaduna su kawo Mani takardar neman biyan kudi duk wannan fa an yi ne su na cikin gida na kyauta ban taba karbar ko sisin Kwabo ba”, inji Mahadi Shehu.
Wannan yasa fitaccen mai kwarmata bayanan yadda al’amura ayyuka  suka kasance a Jihar Katsina da ya kasance haifaffen cikin garin Katsina mazaunin garin Kaduna Dr Mahadi Shehu ya bayyana dalilan da suka sa ya ɗauki matakin rushe gidan Rediyon Vision mai Gajeren Zango da ke Kaduna, a wani taron manema labarai da ya kira a ofishinsa.
Da yake jawabi a lokacin  wani taron manema labarai da ya kira a Kaduna, Mahadi Shehu ya ce ya ɗauki matakin ne saboda ƙarfin da dokar kasa ta bashi a matsayin sa na mamallakin ginin gidan Rediyon, kuma ya bada shi aro ne ga Shugaban gidan Rediyon na Vision wato Umar Faruq Musa tun a Shekarar 2018 ba tare da ya nemi a bashi ko sisin kwabo ba.
“Umar Faruq Musa ya koma da baya yana cin duddugena ta hanyar amfani da ake yi da gidan Rediyon Vision na cikin garin Katsina ana cin mutunci na wanda hakan ya saɓa dokar aikin jarida, kuma aka hana ni yin magana domin in kare kai na a gidan rediyon”.
“Duk da ana zagi na ta hanyar yin amfani da wadansu mutanen da ke zuwa gidan rediyon a Katsina da sunan siyasa ko dai wani shirin son zuciya kuma ba a ba ni ko wani daga waje na damar aji ta bakina ko mayar da martani ba, har cewa na yi zan yi wani shiri ta hanyar duk wani bakatsine ya kira waya daga Katsina ko duk mai son jin ba a sin bakina ni ina daga Kaduna amma a kira ayi Mani tambaya in amsa zan biya kudi naira miliyan biyu a shirin awa daya kawai,kamar yadda tun da farko aka ce bayan kwanaki biyu za a ba ni da na ji shuru sai na kira Manajan gidan rediyon a wancan lokaci sai ya gaya Mani cewa an hana ko da shirin minti daya ne ba a amince in yi ba kuma umarni ne daga Abuja”, inji shi.
Ɗan kasuwar ya kara da cewar Shugaban rediyon Vision ya cigaba da keta mishi haddi tare da nuna tamkar babu wata alaƙa da ke tsakanin su, wannan ne ya sanya a matsayin sa na mai ginin da gidan Rediyon yake ya rubuta takardar neman gidan Rediyon ya tashi ya bashi gidansa ta hanyar bada wa’adin shekara guda, amma a wata ziyara da ya kai gidan Rediyon sai yaga babu wasu kayayyakin, musamman na Dogon karfen da ake Sanya wa gidan rediyo wanda a zatonsa da akwai shi a kafe a cikin gidan saboda idan da karfe sai an yi wahalar cirewa, saboda haka sai ya mayar da wa’adin zuwa watanni huɗu.
Bayan da wa’adin ya cika Umar Faruq Musa bai tashi ba, hakan ya sanya Mahadi Shehu ya zo a wata rana da farko ya fara cire wadansu abubuwa da shi a matsayinsa na mai gidan ya Sanya su wanda daman can ofishinsa ne kasancewa ya daina amfani da wurin safiya taimaki Umar faruq Musa ya yi gidan rediyo a kan rashin Sani, sai umar faruq Musa ya kai kara wajen kwamishinan yan Sanda na Jihar Kaduna bayan an dauki mataki ba daya ba na a samu a hada su baki daya wuri daya domin aji ta bakin kowa lamari ya ci tura domin ya kai kara cewa Mahadi Shehu ya yi masa kutse a cikin gidan rediyonsa.
Sai dai kuma a dukkanin zama da kwamishinan ‘yan sanda ya yi yunkurin yi a tsakanin Mahadi Shehu da Umar Faruq Musa bisa ga ƙarar da shi ya kai abin ya gagara, sakamakon kin yarda su hadu da Mahadin.
Wanda hakan Mahadi Shehu kamar yadda ya shaidawa yan jarida sai ya dauki matakin zuwa gidan ya cire wato yaye kwanon rufin gidan da sili domin kamar yadda ya shaidawa manema labaran rufin kwanon gidan ya tsufa tsawon shekaru 10 da suka wuce don haka ya na bukatar canza sabon rufin gidan baki daya, a matsayin kayansa da ya mallaka.
Daga ƙarshe Mahadi Shehu ya yi amfani da damar da doka ta bashi ya rusa wani sashi na ginin gidan Rediyon, kuma zai kara ɗaukar matakin da ya fi haka matuƙar Umar Faruq Musa bai tashi daga cikin ginin ba.
“Duk da na san abin da dokar kasa ta ce ka yi idan ka ba mutum gida kyauta ya zauna a duk lokacin da kake bukatar gidanka”, inji Mahadi Shehu.
Zaku ga hotunan ginin gidan da kuma takardar da Umar Faruq Musa ya rubuta wa Mahadi ta amsar cewa wannan gidan na Dokta Mahadi Shehu ne.
Don haka ku ci gaba da bibiyarmu domin za mu kawo maku irin yadda yakasance game da lamarin a nan gaba.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.