Home / Kasuwanci / DAMAN NI DAN KASUWA NE ZAN CI GABA DA KASUWANCI NA – MATAWALLE

DAMAN NI DAN KASUWA NE ZAN CI GABA DA KASUWANCI NA – MATAWALLE

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle ya bayyana cewa tun da daman can shi dan kasuwa ne zai ci gaba ne da harkokinsa na kasuwanci kamar yadda ya saba.

Gwamna Muhammad Bello Matawalle ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyon da aka yada wa duniya lokacin da aka yi masa tambayoyi.

Matawalle ya kuma yi wa al’ummar Jihar Zamfara godiya da suka bashi damar jagorantar Jihar

“Kuma ina yi wa jama’ar Jihar Zamfara fatan alkairi baki dayansu. A game da batun matsalar tsaro kuwa ya ce hakika Allah ya Sani ya yi iyakar bakin kokarinsa don haka ina fatan Allah ya kawo karshen ta baki daya”.

Kamar dai yadda kowa ya sani tun bayan kammala zaben Gwamnoni da ya ba jam’iyyar PDP dama a Jihar Zamfara, jama’a na ta fadin albarkacin bakinsu na yin tambayoyi a kan bukatar da ke akwai na jin abin da Gwamna mai barin Gado a Jihar Zamfara Bello Muhammad Matawalle zai fadi don haka wannan zai iya zama biyan bukatar abin da jama’a ke bukatar ji kenan kawai daga bakin wanda ake jiran jin ta bakinsa.

About andiya

Check Also

Kaduna Church Leaders Visit Imams at Eid Praying Ground to Promote Peace, Love, and Religious Tolerance

    In a remarkable demonstration of interfaith harmony, Pastor (Dr.) Yohanna Buru, a Christian …

Leave a Reply

Your email address will not be published.