Honarabul Auwalu Yahaya da ake yi wa lakabi da Yaro Mai kyau na mazabar Unguwar Sanusi da ke karamar hukumar Kaduna ta Kudu ya bayyana cewa dukkan abubuwan da yake yi domin inganta rayuwar jama’a yardar Allah ce ba wai dabararsa ba ko iyawa.
Dan majalisar Jihar Auwalu Yahaya, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen wani gagarumin taron kaddamar da bayar da fom na dalibai 120 da ya biyawa kudin jarabawar WAEC da NECO da suka fito daga mazabarsa ta Unguwar Sanusi a karamar hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna.
Auwal Yahaya, ya ce irin wannan kokarin da yake aiwatarwa ya na yin sa ne a tsawon shekaru 9 da suka gabata da nufin kokarin inganta rayuwar jama’a musamman ma matasa ta fuskar karatu.
“Mun dauki nauyin mata da yawa da suka koyi sana’ar Girke- girke kuma a halin yanzu sun samu sana’ar yi, mun kuma biyawa mutane da dama kudin jarabawar hukumar shirya jarabawa ta NBAIS da suka fito daga makarantun Islamiyya daban daban ta hannun Limaman Masallatan Juma’a da ake da su a Gundumar Unguwar Sanusi a karamar hukumar Kaduna ta Kudu, min kuma raba wa jama’a kyautar motoci sama da 20, wanda yaran nan marasa karfi ne da ba su da galihu a cikin al’umma da wasu ma marayu ne”, inji Auwal Yaro mai kyau.
Sai dai dan majalisa Auwalu Yaro Mai kyau ya bayyana cewa shi a matsayinsa ya na ganin bai dace ba a ce makarantar da marigayi Alhaji Ahmadu Chanchangi ya kafa ta samu nakasu musamman ta fuskar jarabawar fita makarantar Sakandare da ake kira WAEC da NECO, don haka yake yin kira ga jama’a musamman wadanda suka amfana da hankalinsu ya dawo wajen kokarin taimakawa makarantar da dukkan daliban ta kamar yadda lamarin yake a lokacin marigayi Ahmadu Chanchangi da ya samar da makarantar.
Yara sana da dari ya dauki nauyin karatunsu a makarantar koyon kiwon lafiya
Kuma a halin yanzu ya biyawa dalibai dari da Ashirin da kuma dalibai Hamsin kudin jarabawar NECO
Ko a shekarar bara ma dalibai sama da dari kudin WEAC sannan ya biya wa masu rubuta jarabawar NBTE duk suna godiya
Dawainiyar dalibai masu karatun makarantun lafiya da na Jinya da Unguwar Zoma 323 da masu koyon aikin Girke – girke a makarantun
Keken dinki 400, injunan Nika 100 ga kuma rijunan burtsatse masu amfani da hasken rana, tituna a kalla 8 domin jama’a su samu sukunin gudanar da ayyukansu
A gwamnatance an yi aiki a makarantar Firamare Kurmin Mashi a makewayi da Ajujuwa, sai aiki a Makarantar Maimuna gwarzo da makarantar layin Faki, ya na kuma daukar nauyi a duk lokacin da aka samu wata Annoba
Alhaji Honarabul Auwalu Yahaya da ake wa lakabi da Yaro Mai kyau, ya kasance a koda yaushe ya kasance Mutumin mutane da baya gudu ko Kwamar jama’a
Jawabi daga iyalan marigayi Alhaji Ahmadu Cancangi sun ce
Dokta Shaikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce hakika wannan al’amarin ayyuka na Honarabul Auwalu Yaro mai kyau ba wani bakon al’amari ba ne don haka Hakika wannan bawan Allah wakilin ne na gari domin wannan dan majalisa ne ya dauki nauyin fannin makarantar Sakandaren Gumi kwalej ya na daukar dawainiyar a kalla dalibai sama da dari duk ya dauki nauyin a kafarsa.
Kuma za a Farfado da makarantar kiwon lafiya da wanda ya assasa makarantar daman hakan na daya daga cikin niyyarsa
Marigayi Alhaji Ahmadu Cancangi ne ke daukar nauyin wannan makaranta da Shaikh Abubakar Gumi kolej an samar da ita ce domin taimakawa al’umma Maza da mata.
Alhaji Honarabul Auwal Yahaya Yaro Mai kyau tun shekarar 2018 da ka yi masa waya a kan halin da makarantar Gumi kwalej ke ciki nan take ya ce zai yi kuma tun a wannan shekarar Bai fasa ba kowace
shekara sai ya dauki nauyin dalibai
An yaye dalibai sama da miliyan biyar amma ba wanda ke waiwayar makarantar nan sam
Wani ma Daraktan makarantar Anti Nicas, Ibrahim Abdurrashid, ya ce a kowace shekara Honarabul Auwalu Yaro mai kyau na daukar nauyin yara dalibai marayu da marasa karfi a kowace shekara ana biyawa dalibai kudin jarabawar fita Sakandare a makarantar.
Ibrahim Garba, makarantar Irshad remedial and health sciences,hakika Auwalu Yaro Mai kyau na Tallafawa makarantar da ake yi wa horas da daliban a koda yaushe baya gajiyawa
Shima Yusuf Nadabo dan Kantoma, ya ce duk abin da wannan dan majalisar ke yi bai zo da mamaki ba domin shi a koda yaushe ya na kokarin ganin an inganta rayuwar jama’a ne ta kowace fuska.
Musamman ya na kokarin a samu kawar da jahilci a cikin al’umma muna yin addu’ar Allah ya kara fadada masa ya yi abin da ya wuce abin da yake yi
Hukumar Huzba ma sun tabbatar da irin gudunmawar da yake ba su domin samun ingantawar rayuwar jama’a da kuma ganin al’amura sun ci gaba.
Shaikh Nuraini Ashafa shugaban Limaman Masallatan Juma’a a Gundumar Unguwar Sanusi, cewa ya yi hakika Auwalu Yaro Mai kyau ya zama Zakaran Gwajin dafi a tsakanin dukkan yan siyasa
Mun gani a kasa a dukkan mazabun da ke mazabar Unguwar Sanusi mun shaida duk abin da ya aikata domin ci gaban jama’a, kuma ina gaya maka ka kara kaimi da ci gaba da abin da kake yi domin jama’a ta amfana.
Wakilin Honarabul Muhammad Isa Daura, Babuci, kira ya yi ga wadanda suka amfana da abin arzikin da suka samu wanda da hakan ne za a samu ingantar rayuwa sosai.
Kabiru Yusuf Shema garkuwan tudunwada babba, muna yin addu’ar Allah ya kara ba Honarabul Auwalu Yaro Mai kyau kwarin Gwiwar aikin da yake yi.
Ina kiran jama’a ta gari da su shiga cikin harkokin siyasa su inganta ta yadda al’umma za ta kara inganta.
Honarabul Ibrahim Isma’il,
Kira ya yi ga daukacin zababbu da wadanda Gwamnan Jihar Kaduna ya nada da su yi hanzarin yin koyi da ayyukan alkairin da Honarabul Auwalu Yaro Mai kyau ke aiwatarwa domin jama’a su amfana.
Honarabul Auwalu Yaro Mai kyau, shi kadai ne zaka ga ya na tafiya a kan titi da kafarsa ya na gaisawa da jama’a.
Muhammad Alwazir, Ya na ba Limaman Masallatan Juma’a da kuma kungiyoyin mata masu Da’awa guraben kawo yara masu son rubuta jarabawar NBAIS ba su da hali.
“Idan an yi mutuwa, Daurin Aure duk idan an gaya masa da shi za a yi Jana’iza ba tare da gajiyawa ba.
Longdas Emmanuel, Sakataren kungiyar Kiristoci ta CAN Kurmin Mashi, muna godiya kwarai ga wannan dan majalisa domin bamu ta ba samun dan majalisa kamar ka ba.
“Duk abin da zai yi sai ya tuna da mu babu abin da zai yi sai ya tuna da mu a koda yaushe, muna gaya maka muna tare da kai duk abin da zai yi sai ya hada da kieistocin Badikko da Kurmin Mashi”.
Dokta Muhammad cewa ya yi kowa yaji ya gani irin ayyukan da dan majalisar Inguwar Sanusi ke yi domin mun gani a kasa.
“Ba wai an zabi dan majalisa kawai ba ne domin yaje ya yi doka har sai ga shi ya na taimakawa yara karatu da sana’a, samun takardar shedar kammala karatun WAEC da NECO a Bana an biya dubu Arba’in da biyu 42,000 ga kowane dalibi kuma an biyawa dalibai a kalla yara dalibai mutum 120 kamar yadda ake kaddamarwa a yau”.
“Ka tuna fa abin da kake yi kana taimakawa al’umma ta hanyar gina al’ummar da ka yi, Allah ya kara arziki kada Allah ya gajiyar da kai Honarabul Auwalu Yahaya Yaro Mai kyau, muna kira ga sauran yan majalisa da suyi koyi da abin da wannan dan majalisar ke aikatawa
Dan majalisa Auwal Yahaya, da ake yi wa lakabi da Yaro Mai kyau, ya bayyana wa duniya cewa dukkan abubuwan da yake yi da damar da Allah ya ba mu yardar Ubangiji ce ba wai wayon mu, a wannan makaranta muna da dalibai da yawa da suka zama wani abu
“Muna son wannan makarantar ta zama ta wuce kowace makaranta, a shekarar da ta gabata shugaban makarantar ya ce daliban da suka biya kudin rubuta jarabawar kammala karatun mutum hudu ne kawai sai da muka tallafa muka nemo kudi muka biya wa akalla mutane sama da Saba’in domin a samu ainihin lambar yawan mutanen da suka kamata a bisa doka
“Muna da yara dalibai da yawa masu sana’ar koyon girke girke da suka kasance mata kuma duk sun samu sana’ar dogaro da kansu, kuma mun yi aikin bayar da na’ura mai kwakwalwa a nan Kaduna ta Kudu da garin Zariya lokacin ina mai bayar da shawara ga Gwamna a kan harkokin matasa. Mun kuma raba wa mutane Keken dinki,injunan Nika da sauransu kuma Hajiya Hadiza Bala Usman ce ta ba ni ya na a shugaban hukumar kula da zirga zirgar Jiragen ruwan Najeriya, mun bayar da mutane 270 aka dauke su aikin hukumar KASTELA, mun kuma samawa masu kula da Gandun daji wanda Gwamna Uba Sani ya ce a sa suna na domin aba yara dalibai”.
“Na samu tsohon minista a Abuja na ce masa ko’ina ana yin tituna na same shi a Abuja ya kuma ba ni tituna da yawa an kuma yi titunan ga su nan ana ganinsu jama’a na amfana, abin da muka yi na biyawa yara kudin jarabawar WAEC da NECO filina na sayar na biya wa dalibai kudin makaranta.
Muna yin kira ga jama’a da kowa ya yi hakuri ,muna kuma yin godiya ga kowa ina godiya kwarai.