Home / Labarai / Dan Wasan Shirin Kwana Chasa’in Ya Zama Shugaban Sashin Hausa A Kwalejin Ilimi

Dan Wasan Shirin Kwana Chasa’in Ya Zama Shugaban Sashin Hausa A Kwalejin Ilimi

Daga Abubakar Sadiq Mohd, Zaria
Sakamakon wasu canje canjen  da aka gudanar a kwalejin ilmi ta tarayya da ke Zariya,Jihar kaduna Wanda a ciki ma har ya yi awon gaba da Shugaban kwalejin,Dokta Ango Abdullahi Kadan,yanzu haka shi kuma da ya daga cikin yan Wasan kwaikwayon na kayataccen shirin da gidan talabijin na Arewa 24 yake gudanarwa da aka fi sani da suna Hon.Madatai ya zama Shugaban Sashen Koyar da Harshen Hausa na kwalejin.
Dokta .Ahmed S.Bello Wanda dama malami ne a wannan Sashen,kafin zamanshi Shugaba,shine kuma Babban Shugaban Gidan radiyon kwalejin Mai aman sauti watau FCE Zariya FM.
Har ila yau Honarabul Madatai ya rike mukamin mataimakin darakta na Sashen tuntuba na kwalejin (Consultancy Services).
Sabon Shugaban Sashen Koyar da Harshen Hausan da aka haifa a garin Wudil jihar Kano a shekarar 1973,ya kasance gwarzo ta fuskar finafinan Hausa Wanda tun kafin a fara gudanar da shirin Kwana Chasa’in yana fitowa a wasannin Hausa iri dabam dabam, Kamar fim din Doya da Manja, Gida da Waje, Bakin Daji da sauransu.
Dr.A.S Bello yayi digirinsa na farko a Jami’ar Bayero dake Kano inda ya karanta aikin Jarida,ya kuma karanci Harshen Hausa a digirinshi na biyu,sailin da a digirin sa na uku ya kware ta fuskar shiryawa da daukar finafinan Hausa.
A wata zantawa da yayi da manema labarin a Zaria,jim kadan bayan tabbatar Masa da sabon mukamin,Dr.Ahmed S.Bello ya sha alwashin farfado da martaba da darajar Sashen ta yadda kowa zaiyi alfahari dashi.
Ya kuma yi alkawarin tafiya da kowa da kowa don a gudu tare a tsira tare.
Dr.Bello ya kuma shawarci dalibai da su Kara zage damtse domin fuskanta karatun su ka’in da na’in domin kuwa “A wannan karo,ba sa ni ba sabon”.
Yayi gargadin cewa duk dalibin da bai mayar da hankali wajen abinda ake koyar dashi ba,to daga karshe ya koka da kan sa.Domin kuwa a cewarsa “wannan karon ba sani ba sabon”.
Shugaban Sashen sai kuma ya roki malamai da ma’aikatan da su zo a tafi tare su kuma bashi cikakken goyon bayar da hadin kai don sauke nauyin da aka dora mashi ciki.
Ya yi godiya ga hukumar kwalejin ilmi ta tarayya da ke Zariya bisa zabar shi ya Shugabanci Sashen,inda ya bada tabbacin zage damtse don baiwa maras da kunya.

About andiya

Check Also

An Bukaci Yayan Jam’iyyar APC Da Su Ci Gaba Da Zama Tsintsiya Madaurinki Daya

….Lukman Ya Daina Surutu, A bari Majalisa ta yi aikin ta Daga Imrana Abdullahi Shugaban …

Leave a Reply

Your email address will not be published.