Home / Labarai / Daya Daga Cikin Masu Zaben Sarki Na Masarautar Zazzau Sani Aliyu Ya Rasu

Daya Daga Cikin Masu Zaben Sarki Na Masarautar Zazzau Sani Aliyu Ya Rasu

 
Mustapha Imrana Abdullahi

Wani fitacce daga cikin masu zaben Sarki a masarautar Zazzau, Limamin Konan Zazzau Malam Sani Aliyu ya rasu.

A cikin wata takardar sanarwar da ke dauke da sa hannun mai magana da yawun masarautar Abdullahi Aliyu Kwarbai, ta bayyana rasuwar Limamin a daren yau Alhamis.

“Allah ya yi wa Limamin Konan Zazzau rasuwa Malam Sani Aliyu, daya daga cikin mutane biyar masu zaben Sarki a masarautar Zazzau wanda shi ne babban Limamin masarautar”, inji sanarwar.

Sanarwar ta bayyana cewa za a yi Jana’izarsa da karfe Sha daya na safiyar Gobe Juma’a 30 ga watan Yuli, 2021.

About andiya

Check Also

Trafficking: NAPTIP seeks more collaboration, advise potential victims

  By Suleiman Adamu, Sokoto The National Agency for the Prohibition of Trafficking in Person(NAPTIP) …

Leave a Reply

Your email address will not be published.