Daga Imrana Abdullahi
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin DCG Adeniyi Bashir Adewale a matsayin mukaddashin Kwanturolan Hukumar Kwastam na Najeriya.
Sanarwar mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai na sakataren gwamnatin tarayya ce ta bayyana hakan.
Kafin dai wannan nadin Adeniyi (MFR) ACG Adewalw Adeniyi MFR ya rike mukamin kakakin hukumar ta Kwastam kusan shekaru ashirin har zuwa watan Janairun 2017 inda aka mayar da shi rundunar yankin Apapa.
An kara masa girma zuwa mukamin Kwanturola a shekarar 2017 kuma ya zama mataimakin kwamandan hukumar.
Hukumar Kwastam ta Najeriya da ke Gwagwalada, Abuja.A shekarar 2019 aka sake tura shi aiki a matsayin Kwanturola mai kula da filin jirgin sama na Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas.
An kara masa girma zuwa mukamin Mataimakin Kwanturola Janar ne a watan Fabrairun 2020 jim kadan bayan ya sa ido a kan kama wasu kudade da suka kai dalar Amurka miliyan 8.07 da ake kwashewa daga Najeriya ba bisa ka’ida ba ta hanyar E-Wing na tashar jirgin kasa da kasa.
Daga nan ne aka nada shi shugaban hukumar kwastam ta Najeriya da ke Gwagwalada, Abuja a matsayin kwamanda.Binciken karrama sa na kasa (MFR) da aka gudanar a ranar 11 ga watan Oktoba a fadar gwamnati da ke Abuja.
Daukacin ma’aikata da masu taimakawa jaridar theshieldg.com da ke a yanar Gizo na taya wannan sabon shugaban hukumar kwastan murna da fatan Allah ya taya riko, yadda aka hau kan kujerar lafiya Allah kuma ya Sanya a kammala aikin lafiya.