Home / Lafiya / Direban Da Ya Tuka Bature Mai Dauke Da Cutar Coronavirus Ya Gudu

Direban Da Ya Tuka Bature Mai Dauke Da Cutar Coronavirus Ya Gudu

Ana kara fadakarwa tare da bayyanawa daukacin yan Nijeriya cewa suyi hankali da tsananin kula da hanyoyin kiyaye tsafatar lafiyarsu saboda wani al’amarin da ya faru a kasar nan kasancewar wani Bakon da ya shigo Nijeriya aka same shi dauke da cutar coronavirus a yanzu rahotanni na cewa Direban da ya tuka wannan bakon yanzu ya gudu daga wurin da ake tsare da shi ana duba tafiyarsa.

Yanzu-yanzu: Direban da ya tuka Bature mai Coronavirus ya gudu daga asibiti ya ce sai ya yada cutar ko ina a cikin kasar baki daya idan ba a biya masa bukatar ba, kamar yadda rahoton da muka samu ya bayyana.

Wani labari da muka samu yanzu ya bayyana cewa direban motar da ya tuka Baturen kasar Italiya wanda ke dauke da cutar Coronavirus zuwa kamfani a jihar Ogun ya gudu daga asibiti.

Direban an same shi dauke da cutar, amma ya gudu daga asibiti inda yayi barazanar yada cutar a fadin Najeriya idan har ba a bawa dangin shi naira miliyan dari ba (N100m).

Direban mai suna Adewale Isaac Olorogun, bayan wasan buya da ya dinga da gwamnatin jihar ta Ogun, a karshe an samu damar kama shi an kuma samu cutar a jikinshi, amma kafin su fara daukar wani mataki a kanshi har ya gudu daga asibitin.

Bayan guduwar shi ya aika da sako zuwa ga kwamishinan lafiya na jihar, inda ya ce, ba kai daya ne zaka ci kudin ba, yanzu lokacine da dangina za su ci suma, ko ka biya ko ka mutu, zan dinga yadawa mutane cutar a ko ina a fadin Najeriya.

A karshe ya ce yana fatan zai ga shugaba Buhari ya rungume shi.

Kamar yadda shafin AIT Nigeria ya wallafa a Facebook, an bukaci mutane da su dinga lura da irin mutanen da suke zama da su a cikin ababen hawa, sannan kuma a lura idan mutum yayi kokarin rungume ka.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.