Home / Kasuwanci / An Bude Kasuwar Duniya Ta Kaduna Karo Na 41

An Bude Kasuwar Duniya Ta Kaduna Karo Na 41

Daga Imrana Abdullahi Kaduna

Ministan Ma’aikatar ciniki, masana’antu da zuba jari na tarayyar Nijeriya Otunba Niyi Adebayo, ya bayyana Gwamnatin kasar karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin gwamnatin da take kokari matuka domin kawar da duk wata matsala a harkar tsaro.
Minista Otumba Niyi Adebayo ya bayyan hakan ne a wajen taron bude kasuwar duniya ta kasa da kasa da ke Kaduna karo na 41 da ke ci a garin kaduna arewacin tarayyar Nijeriya.
Minista Otumba ya fayyacewa jama’a cewa Gwamnatin na yin wannan kokari ne domin ganin harkokin kasuwanci da tattalin arzikin kasa sun ci gaba da bunkasa.
“Hakika ana samun karin bunkasar harkokin masana’antu tare da bunkasar harkokin kasuwanci da kuma samun gagarumin tagomashi saga kasashen duniya wanda a yanzu ana samun karuwar kasashen duniya masu son yin huldar kasuwanci da Nijeriya wanda hakan ci gaba ne kwarai”.
Ministan ya bayyana cewa kokarin bunkasa tattalin arzikin kasa ne yasa Gwamnatin Nijeriya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta Sanya batun bunkasa tattalin arzikin kasa a matsayin na uku a jerin kudirorinta, hakan yasa da yawa daga cikin kasashen duniya suke fafutukar yin hulda da Nijeriya karkashin Muhammadu Buhari.
Minista Otumba Niyi Adebayo ya kara da cewa taken kasuwar na bana da aka zaba zai taimakawa kokarin Gwamnatin tarayya ta fuskoki da dama na ciyar da kasa gaba.
Ministan ya kuma fayyace cewa bunkasa harkokin Noma zai ci gaba da samar da ayyukan yi da kuma bunkasar tattalin arzikin kasa Baki daya tare da maganin zaman kashe wando.
Gwamnati karkashin Buhari na martaba da kirkiro sababbin abubuwa na ci gaban kasa ta yadda za a bunkasa tattalin arziki da maganin zaman kashe wando
Ministan ya kuma godewa Gwamnatin Jihar kaduna tare da yabawa cibiyar kula da harkokin kasuwanci ciniki da masana’antu ta kasa da kasa ta kaduna bisa kokarin ci gaba da gudanar da wannan kasuwa a duk shekara.
Ya kuma yabawa dukkan masu halartar wannan kasuwa a duk lokacin da za a yi kasuwar duniya ta kasa da kasa a kaduna.
Da yake gabatar da jawabi a madadin Gwamnan Jihar kaduna kwamishinan ma’aikatar zuba jari da kirkire kirkire na Jihar Kaduna Sama’ila Idris Nyan, ya bayyana Jihar kaduna a matsayin wadda ke kan gaba a jerin jihohi ta fuskar zuba jari da saukin gudanar da kasuwanci.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa Gwamnatin Jihar a koda yaushe na shirye domin karbar dukkan masu son zuba jari a dukkan fannin kasuwanci ko masana’antu domin samar da ci gaban kasa baki daya.
Daga cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsa a wurin taron bude kasuwar karo na 41 sun hada da shugabar cibiyar Hajiya Muhibbat Farida Dankaka, Hajiya Saratu Iya Aliyu da masu wasan koroso da shaman Zazzau da suka yi wa jama’a cajin Batur a wurin taron.
Da kuma halartar kamfanoni da masana’antu daga ciki da wajen Nijeriya domin baje hajarsu a kasuwar.

About andiya

Check Also

RE: ALLEGATION OF EXTORTION BY OFFICER OF THE NGERIA CUSTOMS SERVICE FEDERAL OPERATIONS UNIT ZONE ‘B’ AT MOKWA AXIS OF NIGER STATE

      (1) The Comptroller Federal Operations Unit Zone ‘B’ Kaduna, Comptroller Dalha Wada …

Leave a Reply

Your email address will not be published.