Home / Kasuwanci / Dokar Haramta Yin Achaba Da Babura Ko Keke – Napep Bayna Karfe Tara Na Dare Na Nan Daram

Dokar Haramta Yin Achaba Da Babura Ko Keke – Napep Bayna Karfe Tara Na Dare Na Nan Daram

 Daga Imrana Abdullahi
 Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kwara, Ebunoluwarotimi Adelesi, ya bayar da wata tunatarwa ga masu sana’ar yin okada da masu tuka Keke mai kafa uku a jihar cewa dokar hana gudanar da ayyukansu tsakanin karfe 9 na Dare zuwa karfe 6 na safe na ci gaba da aiki a duk fadin jihar.
 Bayan wani taro da kungiyoyin da ke wakiltan kungiyoyin biyu a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin, kwamishinan ya kara jaddada cewa akwai dokar da gwamnatin jihar ta kafa domin dai – daita ayyukansu a cikin wadannan sa’o’i da aka ambata.
 Rundunar Ta kuma jaddada kudirinta na tabbatar da dokar sosai, sannan ta shawarci shugabannin kungiyar da su gargadi mambobinsu game da shirin rundunar na aiwatar da dokar da kuma gurfanar da duk wanda aka samu da karya domin ya fuskanci hukunci.
 A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Okasanmi Ajayi, ya fitar a Ilorin a Yammacin ranar Asabar, kwamishinan Ebunoluwarotimi ya kuma yi gargadi ga masu aikata laifuka a jihar, inda ya bukace su da su canza hanyarsu ko kuma su fuskanci mummunan sakamako.
 Sanarwar ta kuma ja hankalin ‘yan kasa masu bin doka da oda da su gudanar da ayyukansu na halal ba tare da fargabar tsoratar da masu aikata laifuka ko jami’an tsaro ba.
 Kwamishinan ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa za a yi duk mai yuwuwa wajen ganin an mayar da laifuka da aikata laifuka tarihi a Jihar Kwara da yardar Allah madaukakin sarki, yana mai jaddada cewa hakan ba zai kasance kamar yadda aka saba ba ga wadanda suka karya doka a jihar.

About andiya

Check Also

AGILE project trains 2,400 on schools improvement plans in Sokoto 

By; S. Adamu, Sokoto A socio-education project driven organisation , the Adolescence Girls Initiative for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.