Related Articles
Daga Imrana Abdullahi
A kokarin sa na ci gaba da raya addinin musulunci Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayar da umarnin rushe wani masallaci a garin Shanawa da ke cikin karamar hukumar Shinkafi a Jihar Zamfara domin kara raya addinin musulunci a yankin da Jihar Zamfara baki daya.
Bayanan da muke samu a halin yanzu sun tabbatar mana cewa tuni ma aka fara aikin rushe wannan ginin masallaci domin mayar da shi gini irin na zamani.
Kamar yadda wakilin mu ya ganewa idanunsa a cikin garin Shinkafi hedikwatar karamar hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya yi aikin gina sababbin masallatai da yawa a cikin garin da aka rushe su aka gina sababbi tare da aikin Sanya masu shimfida ta zamani domin ayi Sallah a kuma ji dadin yin bautar Allah madaukakin sarki.
Kuma a yanzu haka bayanan da muke samu shi ne akwai wurare da dama da suke neman irin wannan aikin da Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi Shinkafi Sanya a gaba yake ta aiwatarwa domin Allah.
Kamar dai yadda aka Sani ba kowa ke iya yin irin wannan aikin ba sai wanda ya samu sahalewar Allah madaukain Sarki domin aiki ne ake gudanarwa domin sa.
Fata dai Allah ya saka masa da mafificin alkairinsa amin.