Home / Labarai / Duk Abin Da Ake Yadawa Game Da Rabon Abinci Ba Gaskiya – Amako

Duk Abin Da Ake Yadawa Game Da Rabon Abinci Ba Gaskiya – Amako

Duk Abin Da Ake Yadawa Game Da Rabon Abinci Ba Gaskiya – Amako
Mustapha Imrana Abdullahi
Uwargida Steller Amako, mai ba Gwamnan Jihar Kaduna shawara a kan dangantaka da al’umma kuma Ko- dinetar rabon kayan abincin samawa marasa karfi sauki game da annobar cutar Korona ta shaidawa manema labarai cewa an kawo ta domin jagorancin rabon kayan abinci  a karamar hukumar Chikun, wanda wannan shi ne karo na uku kamar yadda mai rikon kujerar Gwamnan Jihar Kaduna ta bayyana.
Kuma ni a wadancan karon da aka yi rabon abinci a karo na biyu na gudanar da aiki na ne a karamar hukumar Zangon Kataf amma a yanzu aka dawo da ni nan karamar hukumar Chikun domin yin wannan aiki na rabon abincin Korona.
Uwargida Amako, ta ci gaba da bayanin cewa kamar yadda aka tsara za a yi wannan rabon abincin ana son a rabawa ainihin Talakawa ne na gaske wadanda ba za su iya taimakawa kawunansu ba irin su ne ake son su amfana.
“Kuma Gwamna ya ce mana baya son siyasa a cikin wannan abin baya son addini a cikin rabon abincin ko batun dan uwa sam a kawar da kai ayi abin da ya dace kawai, wannan yasa aka kafa kwamiti na wajen mutane 9 da suka hada da Fastoci, limamai tare da Kansilolin yankin ba tare da la’akari da siyasarsu ba”.
Ta ci gaba da bayanin cewa amma idan unguwa da akwai Kirista da musulmai to za a samu Fasto daya da Limami daya domin a gudanar da rabon, an kuma Sanya wakilan mata guda biyu a ciki sai aka kawo sarakuna masu unguwanni aka duba wane ne da Kashma da aka ce su ne za su yi rabon wannan kayan abinci.
Sai muka duba shin ina ne za ayi ajiye  wannan kayan abinci sai muka duba wurare hudu mun duba Unguwar Talbijin wato mazabar Yalwa kenan sai muka duba idan mun ajiye a wurin za a samu matsala kuma mun duba zuwa a ajiye a Sabon Tasha nan ma zai zama akwai matsala kuma ba a yarda a ajiye a gudan wani ba saboda haka muka ce to, tun da duk inda muka lissafa mu ajiye muka ga ba zamu yi amfani da su ba.
Sai muka ce to, me ya kamata muyi sai muka ce mu koma mu ajiye a Unguwar Barnawa a layin Gwari domin an yi amfani da wurin a can baya da aka yi rabon kayan abincin karo na biyu.
Sai muka je wurin kwamishinan kula da kasafin kudi da tsare tsare domin shi ne ya yi hanyar samun wurin tun farko, nan da nan kuma muka samu wurin ba komai, sai ya ce ai duk abin da ya shafi Gwamnatin Malam Nasiru Ahmad El – Rufa’i batu ne kawai na Talakawa don haka ba damuwa.
” Mun fara karbar kayan mun gama a ranar 8 ga wannan watan na Goma domin an tsara karbar kayan ne a lokaci daya sannan a kaddamar da rabon kayan a rana daya kada a samu matsalar korafin wasu su ce ta yaya ana rabon kaya a wuri kaza da kaza mu ba a yi a karamar hukumarmu?
Ta ce ba gaskiya ba ne batun yin sama da fadi a boye abinci zance ne kawai irin na mutane kawai dominion zuciya wai an boye abinci idan zaben kananan hukumomi yazo ayi siyasa da shi sam ba gaskiya a ciki.
“Gwamna ya ce kowa ya cire zuciya a kan abincin nan don haka ba batun siyasa a ciki kada ya siyasa su sa hannu a cikin wannan kayan abincin don haka duk karya ne kawai”. Inji ta.
Game da batun abinci mai gaba ta ce abincin da za su raba ba illa a cikinsa, amma na wanda wasu suka je suka balle wurin ajiya a Kakuri masu shi sun tabbatarwa Gwamnati cewa akwai guba a ciki domin ajiyar da suka yi  wa kayan nasu kuma Gwamnatin tuni ta je aka Gwada shi an tabbatar akwai illa don haka ya rage ga wanda ya ci abincin.
Ta kuma yi kira ga jama’a da su guji aikata halaye irin wannan domin abin da hakuri bai ba mutum ba to rashin hakuri ba zai ba mutum ba sam, muna kuma roko ga Gwamna ya duba mu da idanun rahama ya taimaka mana kuma domin duk wanda ya haifi yaya za a samu masu kyau da sabanin hakan

About andiya

Check Also

PDP Youth Leader Commends Hon Umar Yabo

The People’s Democratic Party ( PDP) Northwest Zonal Youth leader Alhaji Atiku Muhammad Yabo, the …

Leave a Reply

Your email address will not be published.