Home / KUNGIYOYI / El-Rufai Ya Yaba Da Zuwan Rundunar Tsaron Sojan Sama Ta Musamman Kudancin Kaduna

El-Rufai Ya Yaba Da Zuwan Rundunar Tsaron Sojan Sama Ta Musamman Kudancin Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i, ya yabawa rundunar sojojin saman Nijeriya bisa yadda suka tura jami’ansu zuwa yankin Kudancin Kaduna domin tabbatar da tsaro.
Su dai wadannan jami’an tsaron sojojin sama yazo ne jim kadan bayan da rundunar sojan kasa suka kai jami’ansu Kafanchan a ranar satin da ya gabata.
Samuel Aruwan, Kwamishina ne mai kula da harkokin cikin gida da tsaro ne ya sanyawa sanarwar hannu.
Gwamnan ya bayyana cewa ya samu wannan labari ne na kai jami’an tsaron sojojin sama na musamman cike da murna da farin ciki.
“ Wannan yunkuri dai ya nuna irin yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari, Gwamna El-Rufa’I, hedikwatar tsaro ta kasa karkashin jajirtaccen jagoransu da kuma shugaban rundunar tsaron sojojin sama”.
“Muna kokarin haduwa da wadannan jami’an tsaron sojojin sama bayan sun kammala tsare tsarensu”.

About andiya

Check Also

Gwamnatin Hadin Kan Jama’a Na Haifar Mana Da Nasara – Gwamna Uba Sani

  …Nan da Sati biyu za a fara aikin garin Tudun biri Daga Imrana Abdullahi …

Leave a Reply

Your email address will not be published.