Home / Labarai / El – Rufa’I Zai Rusa Kaddarori, Ya Kwace Takardun Mallakar Kaddarorin Makarfi

El – Rufa’I Zai Rusa Kaddarori, Ya Kwace Takardun Mallakar Kaddarorin Makarfi

Daga Imrana Abdullahi
GWAMNAN Jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufai, ya kwace takardar mallakar filin da Gwamnatin Jihar ta ba tsohon Gwamnan Kaduna Alhaji Ahmad Muhammad Makarfi na Kaddarori guda Tara (9).
Su dai wadannan Kaddarori na tsohon Gwamna Makarfi tuni har an yi masu lambar za a rushe su gaba daya.
Sanarwar takardar soke takardar mallakar da aka ba shi tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Ahmad Muhammad Makarfi, tuni aka mikawa mahukuntan wadannan kaddarorin a ranar Alhamis, a garin Kaduna.
Takardar sokewar dai na dauke da sa hannun Muhammad Aminu Magatakardar ma’aikatar da ke kula da harkokin Filaye a Jihar Kaduna (KADGIS), an dai rubutawa Ibrahim Makarfi takardar ne Darakta a kamfanin Canes da ke kula da kaddarorin,da ke a harabar Dandalin Murtala mai dauke da lambar filoti 11 a unguwar Doka cikin garin Kaduna.
Kaddarorin da abin ya shafa sun hada da fulotai huda biyar a Magadishu, sai filotai uku a kan Latin Kwato da kuma filoti daya a Doka? dukkansu a cikin garin Kaduna.
“An ba ni umarni ne da in rubuta takarda game da damar mallakar Filaye in kuma sanar da kai cewa Gwamnan Kaduna ya ce a cikin irin ikon da doka ta bashi karkashin sashe na 28 kuma biyar cikin baka (5) (a) da (b) na dokar amfani da fili ta shekarar 1978, ya kwace ya kuma soke damar mallakar da kake da ita”, takardar ta bafface haman karara.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.