Home / Labarai / Ma’aikata Ba Su Taimakawa Gwamnati A Zamfara

Ma’aikata Ba Su Taimakawa Gwamnati A Zamfara

Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Zamfara Alhaji Muhammad Bello Matawalle, ya bayyana cewa in har ma’aikatan Gwamnatin Jihar Zamfara na son karin albashi ya dace su rika taimakawa Gwamnati domin al’amura su ta fi kamar yadda ya dace.
Gwamnan na amsa tambaya ne game da batun karin Albashi inda ya ce ya dace ma daukacin Gwamnati ya rika taimakawa Gwamnatin domin a samu ci gaba, “amma sai kaga babu inda ma aikace ke kokarin taimakawa Gwamnati, musamman a game da batun tara kudin shiga”.
“Ni ne kawai ke biyan Albashi a cikin lokaci kafin wata ya kare kowane ma’aikaci zai samu albashinsa, duk ana yin haka ne domin a karfafawa ma’aikata”.
Gwamna Muhammad Bello Matawallen Maradun ya bayyanawa manema labarai cewa ya gina asibitin kwantar da mutane a kalla 20 a kowace mazaba duk domin kara inganta lafiyar jama’a.
Za kuma a dauki matasan da za su aiki a fannin ma’adinai har mutum dubu 70, wannan kari ne a kan irin yadda muke kokarin inganta rayuwar matasa maza da mata da ake ba su dubu 10 ha maza mata kuma dubu 20 domin su samu sana’ar da za su rike kansu.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.