Home / News / Gamayyar Kungiyar Matasan Arewa A Kaduna Sun Mikawa El- Rufa’i Takardar Koke

Gamayyar Kungiyar Matasan Arewa A Kaduna Sun Mikawa El- Rufa’i Takardar Koke

 Imrana Abdullahi
Gamayyar kungiyoyin matasa a Kaduna karkashin abin da suka kira (Kaduna Concerned Groups) sun mikawa Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I takardar kokensu bisa matsalar tsaron da yankin arewacin Nijeriya ke fama da shi.
Gamayyar kungiyoyin matasan dai sun shiga cibiyar manema labarai da ke Kaduna  ne domin bayyanawa manema Labaran aniyarsu ta bayyanawa irin yadda suke ji dangane da abin da yake faruwa na lalacewar harkokin tsaro da kuma tabarbarewar harkokin tsaro a yankin arewacin Nijeriya
Takardar dai sun mikawa kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida Malam Samuel Aruwan ne da yazo harabar cibiyar manema Labaran ta kaduna domin ya karbi takardar ya kaiwa Gwamnan na Kaduna.
Yusuf Amoke na kungiyar Northern Anticurruption Front ne ya yi wa manema labarai jawabin zuwan nasu a madadin daukacin yayan kungiyar da suka halarci kwaryakwaryan taron.
Sai kuma sauran kungiyoyin da suka halarta sun hada da Jibril Madu Gazama saga kungiyar Arewa Liberation, Aminu Kyari daga kungiyar Kaduna Agenda.
Kwamared  Sa’adu Bako shugaban Youth awareness and mobilization Forum of Nigeria da kuma kwamared Muktar Muhammad shugaban kaduna concerned Youth
An dai gangamin cikin nasara an kuma kare kamu lafiya tare da bin dokar yaki da cutar Korona kamar yadda Gwamnati ta shimfida dokar.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.