Home / News / Na Hannun Daman Kwankwaso Ya Koma APC

Na Hannun Daman Kwankwaso Ya Koma APC

Daga Wakilinmu
Wadansu rahotannin da muke samu daga Jihar Kano na cewa Alhaji Dakta Rabi’u Suleiman Bichi, babban na hannun daman Rabi’u Musa Kwankwaso ne amma kuma a halin yanzu bayanan da muke samu daga majiya mai tushe na cewa ya kammala shirye shirye komawa jam’iyyar APC da ke da Gwamnatin Jiihar karkashin Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Kamar yadda zaku iya gani a wannan hoton shi dai Dakta Rabi’u Suleiman Bichi babban na hannun daman Kwankwaso ne wanda ya zama sakataren Gwamnatin Jihar Kano kuma kafin zama sakataren Gwamnati ya rike mukamai da dama a ciki da wajen Jihar Kano.
Sai dai kamar yadda wata jaridar da ake wallafa a yanar Gizo ta ruwaito cewa Dakta Bichi ya dauki wannan mataki ne kasancewar ba ayi da shi sosai wato baya cikin masu fada a ji a bangaren Rabi’u Musa Kwankwaso, duk da cewa shi ne shugaban Jam’iyyar PDP reshen Jihar
Kamar yadda tarihi zai tabbatar cewa ko a Gwamnatin Ganduje ma ya ci gaba da zama sakataren Gwamnatin Jihar Kano bayan an samu farraka tsakanin Ganduje da Kwankwaso.
Wannan shi ne abin da yan magana ke cewa siyasa bata da masoyi ko makiyi na dindindin.

About andiya

Check Also

Edo 2024: Group Hold Symposium In Support Of Asue Ighodalo

  The Good Governance Advocacy Group, has held a symposium to drum their support for …

Leave a Reply

Your email address will not be published.