Home / Lafiya / Gwajin Cutar Korona A Jihar Kaduna Kyauta Ne

Gwajin Cutar Korona A Jihar Kaduna Kyauta Ne

Gwajin Cutar Korona A Jihar Kaduna Kyauta Ne

Mustapha Imrana Abdullahi
Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna Dokta Hadiza Balarabe da Kwamishiniyar lafiyan Jihar kaduna sun tabbatar da cewa yin Gwajin cutar Korona kyauta ne a Jihar kaduna.
Sun tabbatar da hakan ne a wajen wani taron tattaunawa da kafafen rediyo domin yi wa jama’a jawabi a game da halin da ake ciki a kan cutar Korona a duk fadin Jihar.
Sun bayyana cewa an samar da wuraren cibiyoyin tabbatar da mai cutar Korona bayan an yi masa Gwaji har cibiyoyi Takwas kuma ana kokarin samar da wasu a nan gaba.
Mataimakiyar Gwamnan ya bayyana cewa dukkan matakan daraja dauka a lokacin kokarin dakile cutar Korona karon farko kamar Sanya Takunkumin rufe hanci da baki, yanayin daukar fasinjoji a motocin haya da Keke Nafef, kokarin wanke hannu da sauran dukkan matakan da aka dauka a tun farko domin dakile cutar musamman shiga cinkoso.
Ta ci gaba da cewa idan mutum ya fita misali zuwa unguwar Kawo sai kaga mutane basa son Sanya Takunkumi duk da hadarin cutar.
” A lokacin da aka sassauta dokar a Masallatai da Kasuwanni ana kokarin kiyaye matakai amma sai a yanzu aka daina amfani da dokar.
Daga yau an rufe gidajen rawa,
“wasanni,wuraren shakatawa da gidajen giya, amma otal Otal za su ci gaba da sana’arsu tare da kiyaye doka da ka’ida”.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.