YA GAIYACI TSOHUN MAIMAKIN SHUGABAN KASA ALH. ATIKU ABUBAKAR WAZIRIN ADAMAWA.
ABANGARAN MULKINASA DA SAURAN ABUBUWA DADAMA.
Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammed Abdulkadir (Kauran Bauchi) ya samu nasarori da dama a kasa da shekara biyu Babu shakka cewa Sanata Bala Muhammed shi ne almasihu na wannan lokacin a matsayin Gwamna a Jihads Bauchi, bisa dogaro da manufofinsa, a matsayinsa na gwamna, bai bata lokaci ba, amma ya zage damtse da nufin tabbatar da amincewar da aka yi masata masu zabe.
Gwamna Bala Muhammed ya kaddamar da aikin gina titina a yankunan da har zuwa yanzu ba su da hanyoyin shiga tare da gyara wadanda ake da su a babban birnin jihar da sauran shiyyoyin majalisar dattawa a jihar.
Gina tare da gyaran hanyoyi guda hudu da kudinsu ya kai kusan Naira Biliyan Biyar wadanda suka hada da; Ibrahim Bako to Maiduguri road Bye-pass, sabon Kaura zuwa Jos road.
Gwamnan ya kuma bayar da aikin gina titin kilomita 58 da ya hada Yalwan Duguri, Badaran Duste, Birin, Bajama, Kumbala, Kundak Wurno da Burga na kananan hukumomin Tafawa Balewa da Alkaleri, Sade zuwa Akuyam a karamar hukumar Misau GRA Azane zuwa tsohon titin kano
a karamar hukumar Katagum.
Haka kuma Sanata Bala Muhammed bai takaita ayyukan gina tituna a cikin babban birnin ba, amma ya bayar da umarnin gina hanyoyi a wasu kananan hukumomin jihar.
Haka kuma ya nuna cewa a zahiri shi mutum ne na jama’a da ba shi da alaka da jam’iyya ko siyasa, ba tare da addini ko zamantakewa da tattalin arziki ba.
Ya zo ne domin kawo sauyi a jihar Bauchi ta hanyar gyara wasu sassan jihar kamar bunkasa noma a karamar hukumar Zaki da inganta fannin kiwon lafiya a jihar, samar da kayan aikin makaranta musamman makarantun firamare a jihar da kayan aikin fasaha.
Gyara tsarin ruwa a cikin jaha don karfafawa matasa & mata su kasance masu zaman kansu ta fuskar tattalin arziki ko masu dogaro da kai.
Sanata Bala bai tsaya a kan titi ba,gine-gine ya sake gyara wasu sassa amma ya yi kokarin duba jin dadin ma’aikata ta hanyar kafa wani kwamiti da zai duba mafi karancin albashi a wasu domin daga darajar tattalin arzikin ma’aikata da kuma kara yawan ma’aikata a jihar.
Baya ga haka, Sanata Bala Muhammed ya ci gaba da bin diddigin rashin biyan ’yan fansho, inda ya tabbatar da hakan domin botany basussukan da ake binsa, gwamnan ya dauki matakin tantance ma’aikata na gaggawa don zakulo ma’aikatan da suka karbi bakuncinsu, sakamakon gano fatalwa 584. ma’aikata daga cikin ma’aikata dubu 596 da dari shida a jihar.
Sanata Bala Muhammed, saboda hidimar jin kai da kuma kaunar bil’adama ya bayar da afuwar wasu fursunoni a jihar da aka yi musu gyara.
Har ila yau, don neman ilimi ya ba wa ɗalibai guraben karatu da yawa don yin karatu a gida da waje don gina ƙasa.
Gwamnan ya kuma gina azuzuwan karatun Larabci da na Yamma ga Almajirai domin su dace da kuma basu fata na gaba.
A kwanakin baya ne aka tura mutum 25 da suka kammala digirin lantarki da injiniyoyi daga kananan hukumomi 20 zuwa cibiyar horar da wutar lantarki ta kasa ta Najeriya domin ci gaba da karatu a fannin watsa wutar lantarki da rarraba wutar lantarki, inda aka baiwa kowane wanda ya samu horon 750,000 dubu dari bakwai da hamsin da 100,000 da dari don kayan aikin sa.
(SASHEN ILIMI)
A cigaba da bankado’ da koyarwa da Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir yayi a jihar Bauchi undersa na shekarabiyu bisa yadda da sa Kwamrade Mukhtar Gidado (Special Adviser On Media) yau muna Ma’aikatan Ilimi.
A kokarin Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na kawo sauyi kan ilimi tundaga tushe yasa yadakko Kwamishina Mai hazaka wadda yasan aiki.
An cimma abubuwa dayawa a wannan Ma’aikata na ilimi kamar Gyara ajujuwa 360 da Kuma Gina sabbin ajujuwa 240 a Makarantun primary a fadi’n jihar Bauchi, wadda samada Kashi 80% an saka kayan koyo da aiki.
Da kudi’ kadan angyar manyan Makarantu na Sekandiri na musamman wato Special School wadda ayanzu haka an gyara komai a ciki musamman abunda yashafi ajujuwansu, Ruwan Sha, Inganta yadda ake basu abunci da aihin abubuwa da yakamata a wadannan Makarantun.
Akwai Kudiri na Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na gyara manyan Makarantu a kowace karamar hukumar Hukuma a jihar Bauchi, wadda anfara yadda akesa Makaranta daya’-daya’ a cikin kasafi na Shekara da akeyi Kuma aiki na tafiya yadda aka tsara nasu da saka kayan koyo da kariya da ingantasu da gyaran Malamai (Staff Quarters) a duk manyan Makarantunmu dasuke Kananan fur a jihar.
Hadin tsakanin Gwamnatin jihar Bauchi da Bankin bunkasa Africa (ADB) wadda suke Kan gina sabbin Makarantu a mazabun Sanatoti na jihar Bauchi wadda akwai daya’a Dagauda daya’a Mashema wadda aikin yakai 90% na kammalawa.
Tabbatar da bin aihin tsari na koyo da jagoranci a duka Makarantunmu.
Bin ka’ida da aihin bin tsari na biyan kudin jarabawa na NECO, da JAMB wa dalibai dasuka chanchanta a biya musu don kara musu karfin sabanin yadda akeyi abaya.
Babu Ma’aikatan da take da aihin jadawali na Ma’aikatanta kamar Ma’aikatan ilimi lura da yadda ma’aikatan ke aiki babu wasa wadda a yanxu haka babu wani ghost Worker a wannan Ma’aikata.
A kokarin Gwamnatin jihar Bauchi na Samar da dawwamammen tsari ta dauki alamar na digitalising daukan rahoto na duk malamin da yake jagoranci a duka Makarantun Gwamnati wadda an dauki Ma’aikata na Wucin gadi wadda zasu dunga daukan bayanin malami in yashiga aji da lokacin tashinsa a yanxu haka ana cigaba da wannan tsari.
Ba’a tsaya anan ba lura da Mahimmancin ilimi Gwamna ya amince da biyan dukkan hakkokiin malamai da Karin girma nasu a lokacin da yadace.
Shirin bada ilimi kyauta wa mutanen yankin Karkashin shirin BESDA wadda hada’kace da ilimi bai daya’ na UBEC, an Gina Makarantu na Wucin gadi da bandaki da Ruwa mai tsafta a wuraren da kuma biyan wadda ake koya musu karatun don sudage su Yakijahilci.
An kuma raba kayan koyo da tsare tsare UBEC wa Kananan Makarantu hadda kekuna na guragu don Basu damar zuwa Makaranta kamar yadda masu kaga ke zuwa.
-A yanzu haka Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir yasaka Kason Gwamnatin jiha a Maganar UBEC na zimmar kudi’ 1.66billion na wannan Lokaci
(TAIMAKON RAYUWAR MARAYU DA MARASA GALIHU)
Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir karkashin Gwamnatin sa ansamu aikin dayawa a cikin Kasa da shekara biyu.
Sanin kowane a fadi’n Nigeria Babu wata jiha da Ma’aikatan jihar suka bada Kashi 1% na hidimansu don inganta rayuwar Marayu da wasan galihu a hukumance sai jihar Bauchi.
Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir yabada dama wa Shugaban Magana BASOVCA wajen ganin an kafa wa Iyayen marayun da kayan Sana’a don su rike marayun dasuke kusa dasu, Akan ace a kashe wa maraya ba, don itama uwar marayar tasamu damar tsare mutuncinta wajentadakai.
A yunkurin Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na ganin an samu damar Kara yawan dalibai marayu a Gwamnatin baya Marayu 3000 ne suka samu dama a shekara Hudu da Gwamnatin Baya suka yi anfana aka daukesu karatu, Amma a yanzu haka kasa shekara biyu munada dalibai 4000 wannan bakaramin hubbasa bane. da nasara a Gwamantin kaura.
-A yanxu haka ta fadada’aikin ta zuwa kananan 20 sabanin yadda yake ada kananan 12 ne lura da yadda wannan kudi’ a na cire wa duk Ma’aikatan Gwamanti ne tunda kowace karamar hukumar Hukuma akwai Ma’aikatan Gwamnati yasa maigirma Gwamna yayi Umurnin a fada’da’.
A kokarin Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir yabada dama wa hukumar BASOVCA da gyara Gidajen marayu wadda suke cikin matsananciyar bukata na rushewar gida ko rashin lafiya.
Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir ya rattaba hanu kan dokan cin damar yara (VAPP LAW) don kare hakkin marayu da ake cin damar su.
Wannan hukumar na BASOVCA Bata tsaya anan ba tana taimaka wa al’umma wajen rashin lafiya musamman masu dauke da chututtuka musamman wadanda suke wuraren.
A Gwamnatin Kaura ansamu damar chanxa yadda ake bada tasirin wa aihin mabukata wajen Yi musu Kai tsaye.
Wadda a yau dinnan 29/05/2021 yagana da aihin Marayu dasuke BASOVCA yaci abunci dasu a Matsayin Ranar Dimokaradiyya na Cika Shekara BIYU dayayi akan karagar mulki.
Da dai sauransu
An yi wasu shugabanni, wasu kuma an haife su, Sanata Bala Mohammed (Kauran Bauchi) haifaffen shugaba ne wanda Allah ya ba shi halaye domin dinke barakar da ke tsakanin masu hannu da shuni da wadanda ba su da su.
Shi shugaba ne mai sha’awa, a zuci da kuma tsayin dakawajan Maginin wasu Bata Gari.
Karshan Rahoton Kenan Jamilu Barau Daga Bauchi