Home / Labarai / Gwamna Buni Ya Yabawa Gwamnatin Tarayya Kan Maido Kudaden Ta, A Matsayin Diyya Na Hanyoyi Da Ta Gina 

Gwamna Buni Ya Yabawa Gwamnatin Tarayya Kan Maido Kudaden Ta, A Matsayin Diyya Na Hanyoyi Da Ta Gina 

 

Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu

 

 

Gwamnan jihar Yobe Hon.  Mai Mala Buni ya yabawa gwamnatin tarayya bisa amincewar  da maido da makudan kudi kimanin Naira biliyan 18 da gwamnatin jihar ta kashe wajen sake gina titunan gwamnatin tarayya guda biyar da ke jihar.

Gwamna Buni ya yi wannan yabon ne a ranar Larabar da ta gabata bayan amincewar da majalisar zartarwa ta tarayya ta yi na mayar wa gwamnatin jihar kudaden.

Ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta yi amfani da kudaden cikin adalci wajen samar da karin ababen more rayuwa a yawancin al’umma a fadin jihar.
.
“A cewarsa, mayar da kudaden zai baiwa gwamnatin jihar damar gudanar da wasu ayyuka da suka shafi jama’a da za su inganta rayuwar al’umma.”

“Ina so in yaba wa shugaban kasa musamman da mambobin majalisar zartarwa ta tarayya bisa yadda suke nuna adalci ga jihar.”

“Alal hakika samun wadannan makudan  kudaden zai ba da gudummawa ga sauran ayyukan da za su yi tasiri ga rayuwar mutanenmu.”

“Gwamnati za ta karkatar da albarkatun zuwa ilimi, samar da kiwon lafiya, samar da ruwan sha, samar da ayyukan yi da sauran ababen more rayuwa domin inganta rayuwar al’ummar mu” Gwamna Buni ya tabbatar.”

Ya bayyana cewa irin wannan fahimtar da ke tsakanin gwamnatocin Jihohi da na tarayya za ta sa gwamnatin jihar za ta kara kaimi wajen aiwatar da ayyukan gwamnatin tarayya da ke da tasiri kai tsaye ga rayuwar al’umma.

Majalisar zartaswa ta tarayya a zamanta karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ta amince wa gwamnatin jihar Yobe Naira biliyan 18 dangane da sake gina  wasu hanyoyin gwamnatin tarayya guda biyar da gwamnatin jihar ta sake gina wa.

About andiya

Check Also

Senator Yar’adua Donates Books To Schools In 11 LGAs

By Lawal Gwanda Senator Abdul’aziz Musa Yar’adua of Katsina Central Senatorial District has donated assorted …

Leave a Reply

Your email address will not be published.