Home / Labarai / Gwamna Dauda Lawal Ya Jajantawa Al’ummar Zurmi Da Birnin Magaji 

Gwamna Dauda Lawal Ya Jajantawa Al’ummar Zurmi Da Birnin Magaji 

Daga Imrana Abdullahi
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal a Juma’ar nan ya ziyarci al’ummomin Ƙananan Hukumomin Zurmi da Birnin Magaji bisa harin ta’addancin da ‘yan bindiga suka kai, inda Gwamnan ya jaddada aniyar sa ta kawo ƙarshen matsalar tsaron da jihar ke fama da shi.
In dai ba a manta ba, a makon da ya gabata ne ‘yan bindiga suka kai hare-hare a Nassarawar Zurmi da ke Ƙaramar Hukumar Zurmi da Nasarawar Godel da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji a cikin jihar ta Zamfara.
A cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu a Gusau yau Juma’a, ya bayyana cewa ziyarar ta kasance ta jaje ce da ta’aziyya ga al’ummar da wannan bala’i ya shafa na asarar rayuka, tare da nuna cewa gwamnati na tare da su.
Ya ce, Gwamnan ya nuna wa jama’ar cewa yana tare da su, ya kuma tabbatar da jajircewar gwamnatin sa wajen lalubo sahihiyar hanyar kawo ƙarshen wannan bala’i da ya addabi jihar.
Sanarwar ta Malam Idria ta kuma bayyana cewa, a yayin da Gwamna Dauda ya kai ziyarar gani da ido ga ofishin ‘yan sanda na Zurmi, wanda ‘yan ta’addan suka ƙona, ya nuna masu a shirye ya ke wajen samar masu da duk kayan aikin da su ke nema don wannan namijin aiki.
Gwamna Lawal ya ce, “Ina miƙa saƙon ta’aziyya ta game da jami’ai biyu da suka rasa rayukan su a harin da ‘yan bindiga suka kai wa Nasarawar Zurmi. Ina sane da irin tashin hankalin da ke tattare da irin wannan bala’i ga duk wanda ta rutsa da shi, ina tabbatar maku, tare da iyalan waɗannan gwaraza, cewa ina tare da duk al’ummar wannan yanki a cikin addu’o’i na.
“Na yi matuƙar jinjina ga ƙoƙarin jajirtattun jami’an tsaron mu masu yaƙi da ta’addanci. Jajircewar ku na ganin kun kare al’ummar mu daga ‘yan ta’adda, wannan abin yabawa ne.
“Gwamnati na za ta ci gaba da bayar da duk wani taimako da dakarun mu ke buƙata. Tare za mu kawo ƙarshen waɗannan matsaloli, kuma mu ƙara ƙarfi.”
A lokacin da Gwamna Lawal ya shiga garin Zurmi, ya kai gaisuwar ban-girma ga Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Sulaiman.
Da ya ke jawabi ga jama’ar Nasarawar Godal da ke Ƙaramar Hukumar Birnin Magaji kuwa, Gwamna Lawal ya tabbatar masu da cewa ya riga ya aiko da kayan tallafi tun lokacin da abin ya faru.
“Na zo yau ne domin in nuna tausayawa ta da ta’aziyya ga iyalan waɗanda wannan abu ya shafa, tare da tabbatar da cewa gwamnati na ba za ta numfasa ba, har sai ta kawo ƙarshen wannan rashin tsaro.
“Ina fata wannan ziyara tawa za ta miƙa wani saƙon kyakkywar fata ga al’ummar Nasarawar, tare da tabbatar masu da cewa muna tare da su a wannan mawiyacin hali.
A lokacin da ya ke dawowa zuwa Gusau, Gwamna Lawal ya ya da zango a Kasuwar Daji da ke Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda don jajanta wa Alhaji Hamisu Kasuwar Daji, wanda waɗannan ‘yan ta’adda suka kai wa gidan sa hari.

About andiya

Check Also

Return Our Property, Documents In Your Possession, SWAN Tells Ex-President Sirawo

    The Sports Writers Association of Nigeria (SWAN) has warned its erstwhile National President, …

Leave a Reply

Your email address will not be published.