Home / Lafiya / Gwamna Dauda Lawal Ya Kaddamar Da Gyara, Inganta wa Da Samar Da Kayan Aiki A Asibitin Kwararru Na Gusau

Gwamna Dauda Lawal Ya Kaddamar Da Gyara, Inganta wa Da Samar Da Kayan Aiki A Asibitin Kwararru Na Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya ƙaddamar da aikin gyara, ingantawa da kuma samar da kayan aiki a cibiyar kula da lafiya ɗaya tilo mallakar gwamnatin jihar, wanda shi ne asibitin ƙwararru na Yariman Bakura da ke Gusau.
An gudanar da bikin ƙaddamarwar ne a ranar Alhamis da ta gabata a asibitin ƙwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura da ke Gusau, babban birnin jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa ingantawar za ta mayar da asibitin zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Jihar Zamfara.
A yayin jawabinsa a wurin taron, Gwamna Lawal ya tabbatar da cewa, gyaran zai inganta tsarin kula da marasa lafiya ta musamman, da ƙara yawan ma’aikatan kiwon lafiya, da kuma inganta tsarin ayyukan, wanda zai haifar da ingantacciyar kiwon lafiya.
“Mun zo nan a yau ne domin ƙaddamar da gyare-gyare da kuma samar da kayan aiki na asibitin ƙwararru na Ahmad Sani Yariman Bakura da ke Gusau. Aikin zai kuma ƙunshi samar da kayan aikin jinya ga asibitin. Wannan aiki dai ya biyo bayan ayyana dokar ta-ɓaci ne a fannin kiwon lafiyar jihar, bayan na ilimi.
“Wannan babban ƙalubale ne da muka gada a wannan fanni lokacin da muka karɓi ragamar mulkin jihar.
“Asibitin na cikin mawuyacin hali duk da irin rawar da yake takawa wajen samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga mazauna da baƙi a jihar bakiɗaya. Yawancin kayan aikinsa sun lalace, wanda hakan ke nuna buƙatar kulawar gaggawa. Bugu da ƙari, asibitin ba shi da isassun kayan aikin ɗakin gwaje-gwaje, wanda ke kawo cikas ga ma’aikatan wajen aiwatar da muhimman hanyoyin gano cututtuka yadda ya kamata.
“Manufarmu ba wai don kare lafiya da jin daɗin mazauna jihar da ma’aikatan kiwon lafiya ba ne kawai, sai dai har da magancewa da shawo kan cututtukan da ke yaɗuwa da kuma waɗanda ba sa yaɗuwa.
“Muna da niyyar samar da cikakkiyar tsarin kula da lafiya wanda zai ƙunshi nau’ikan ayyuka masu muhimmanci, gami da samar da magunguna masu muhimmanci, matakan rigakafi, sake fasalin manufofin kiwon lafiya, aiwatar da ƙa’idoji kan tsaftar ruwa da ƙa’idojin tsabtar muhalli, kula da yanayin kiwon lafiya, shirye-shiryen rigakafi, kula da lafiyar mata masu juna biyu, inganta tsarin abinci mai gina jiki gami da ƙarfafa tsarin ba da gudummawar kuɗaɗen kula da lafiya.
“Kamar yadda Asibitin ƙwararru na Yariman Bakura ya kasance shi ne kaɗai cibiyar kula da lafiya mallakar jihar, akwai buƙatar ya samar da kulawa ta musamman da suka shafi haɗaɗɗun matakan jiyya, tare da ba da horo ga ƙananan likitoci da samar da yanayi mai kyau ga ƙwararrun kiwon lafiya da ke gudanar da bincike a fannonin kiwon lafiya daban-daban. Ya zama wajibi mu tabbatar da sake fasalin asibitin. Mun yi niyyar mayar da Yariman Bakura asibitin koyarwa na Jami’ar Jihar Zamfara da zarar an fara Kwalejin Kimiyyar Lafiya.
“Abubuwan da za a aiwatar da gyaran a kan su za su haɗa da sabbin gine-gine, faɗaɗawa da inganta gine-ginen da ake da su, gyara gine-ginen da ake da su, da kammala rukunin ginin likitoci, da bunƙasa ɗakin gwaje-gwaje. Haɓaka kayayyakin aiki da inganta cikakken tsarin Kula da Bayanan Asibiti.”

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.