Home / Uncategorized / Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Ta’aziyya Tare Da Nuna Alhini Game Da Kwanton Baunar Da Aka Yi Wa Askarawa 

Gwamna Dauda Lawal Ya Yi Ta’aziyya Tare Da Nuna Alhini Game Da Kwanton Baunar Da Aka Yi Wa Askarawa 

A Talatar nan ne Gwamna Dauda Lawal ya yi ta’aziyya, tare da nuna alhinin kwanton ɓaunar da aka yi wa dakarun Askarawan Zamfara na ‘Community Protection Guards’, inda aka kashe wasu daga cikin su a yankin Tsafe ta jihar Zamfara.
Gungun wasu ‘yan bindiga ne suka yi wa Asakarwan kwanton ɓauna a Litinin ɗin nan da ta gabata a wani shingen binciken ababen hawa da aka kafa a Ƙaramar Hukumar Tsafe.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya sanya wa hannu yau a Gusau, ya bayyana cewa Gwamna Lawal ya nuna takaici da baƙin ciki bisa wannan ɗanyen aiki da waɗannan ‘yan bindiga suka aikata, waɗanda ya ce yanzu haka an ci ƙarfin su, suna hanyar guduwa ne.
Daga nan Gwamnan ya jinjina wa Asakarawan, tare da sauran jami’an tsaro bisa sadaukarwar su ta kare rayukan al’umma.
Gwamnan ya ce, “Na samu wani mummunan rahoton kwanton ɓaunar da ‘yan bindiga suka yi jiya a Ƙaramar Hukumar Tsafe, wanda hakan ya yi sandiyyar rasa rayukan gwarazan Askaran Zamfara mutum tara.
“Askarawan da aka yi wa wannan kwanton ɓauna, su ne, Nasiru Aliyu, Jabiru Hassan, Abdullahi Dangude, Bashar Bawa, Mu’azu Musa, Anas Dahiru, Anas Yakubu, Lawali Yunusa da wani mutum ɗaya.
 “Wannan kwanton ɓauna da aka yi wa jami’an mu, aiki ne na matsorata, domin yanzu haka ƙoƙarin guduwa suke yi sakamakon ruwan wutar da su ke sha daga jami’an tsaro a duk faɗin jihar.
“Dakarun jami’an tsaro za su ci gaba da fafarar waɗannan ‘yan bindiga domin karya lagon su a jihar Zamfara da ma yankin baki ɗaya.
“Ina so a madadina da gwamnatin jihar Zamfara in miƙa ta’aziyya ta ga iyalai da dangin waɗannan gwaraza da suka rasa rayukan su. Ba za mu taɓa mantawa da sadaukarwar su ba. Ina kuma addu’ar Allah kawo sauƙi ga waɗanda suka samu raunuka.
“Gwamnatina a shirye ta ke don bayar da duk wata gudumawa ga iyalan waɗannan gwaraza da suka rasa rayukan su.”

About andiya

Check Also

Dangote Hails Tinubu on Impact of Crude for Naira Swap Deal

      …As Dangote Refinery partners MRS to sell PMS at N935 per litre …

Leave a Reply

Your email address will not be published.