Home / Labarai / GWAMNA DAUDA LAWAL YA ZIYARA NEMA, YA NEMI DAUKI NA MUSAMMAN GA ZAMFARA

GWAMNA DAUDA LAWAL YA ZIYARA NEMA, YA NEMI DAUKI NA MUSAMMAN GA ZAMFARA

Daga Imrana Abdullahi

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal, ya yi kira da a kara ba hukumar agajin gaggawa ta kasa (NEMA) tallafi da kuma dauki na musamman ga Jihar Zamfara.

Gwamnan ya yi wannan roko ne a ranar Juma’a a lokacin da ya ziyarci hedikwatar Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da ke Abuja.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce ziyarar ta zo daidai da kudurin gwamna Dauda Lawal na buga duk wata kofa da za ta amfanar da al’ummar Zamfara.

Ya kara da cewa Gwamnan ya samu tarba daga babban daraktan hukumar NEMA, Ahmed Mustapha Habib da sauran manyan jami’an hukumar.

Ya ce: “A kokarinsa na ganin jihar Zamfara ta inganta, Gwamna Dauda Lawal ya ziyarci Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta kasa (NEMA) inda ya nemi karin tallafi da kuma dauki na musamman daga hukumar.

“Gwamnan ya amince cewa jihar Zamfara tana da abubuwa da yawa daga hukumar NEMA ta fuskar bada tallafi na yau da kullun da kuma karfafawa da nufin dawo da martabar ‘yan adam ga ‘yan gudun hijira.

“Na roki Darakta Janar da ya kara yi wa Zamfarawa, la’akari da tattalin arzikin jihar, inda illar ‘yan fashi suka durkusar da harkar noma, kasuwanni, da samar da albarkatu.

“ziyarar gwamna ta kara bayyana cewa jihar Zamfara na bukatar taimakon gwamnatin tarayya, musamman daga hukumomi irin su NEMA, domin karawa gwamnatin jihar damawa.

“Tsarin na musamman ya yanke game da abinci da abubuwan da ba abinci ba, samun fasaha da kayan aikin ƙarfafawa, lafiyar masu tabin hankali, da masu rauni da sauransu.”

Da yake mayar da martani babban daraktan hukumar NEMA Mustapha Habeeb ya godewa gwamna Lawal bisa wannan ziyarar.  Ya yi alkawarin ci gaba da mayar da martani ga halin kuncin da al’ummar jihar Zamfara ke ciki.  “Kun zo nan ne don yin hadin gwiwa da mu, don hada kai da mu,Kofar  NEMA tana bude musabaha na wannan hadin gwiwa.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.