Home / Uncategorized / Gwamna Dauda Na Zamfara Ya Jaddada Kudirinsa Na Bayar Da Tallafi Ga Jami’ar Tarayya Ta Gusau

Gwamna Dauda Na Zamfara Ya Jaddada Kudirinsa Na Bayar Da Tallafi Ga Jami’ar Tarayya Ta Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bayar da duk wani tallafin da ya dace ga Jami’ar Tarayya ta Gusau.
Shugaban Hukumar gudanarwar Jami’ar ta Tarayya da ke Gusau, Rt. Hon. Injiniya Aminu Sani Isa ne ya jagoranci Majalisar Gudanarwar jami’ar a wata ziyarar ban-girma da  suka kai wa Gwamna Dauda Lawal a ofishinsa da ke gidan gwamnati, a ranar Talata.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya ce Majalisar Gudanarwar ta yaba wa gwamnatin jihar bisa goyon bayan da take bai wa jami’ar.
Sanarwar ta ƙara da cewa, yayin da yake mayar da martani ga shugaban jami’ar, Gwamna Dauda Lawal ya yi alƙawarin taimaka wa jami’ar a kodayaushe saboda irin rawar da take takawa wajen ci gaban ilimi.
Gwamnan ya jaddada cewa, gwamnatin jihar za ta ci gaba da haɗa kai da jami’ar domin samun ci gaba mai ɗorewa a fannin ilimi.
“Ina miƙa godiyata ga majalisar gudanarwa ta Jami’ar Tarayya ta Gusau bisa wannan ziyara. Irin wannan ziyara yana ba da damar yin nazari da tsara hanyoyin da za mu inganta fannin ilimi don amfanin jama’armu.
“Na yi farin ciki da jin cewa jami’ar za ta fara bayar da takardar MBBS. Mun kasance kan gaba wajen inganta asibitocinmu zuwa asibitocin koyarwa, don haka za a samu asibitin koyarwa a jami’ar
“Kamar yadda ku ka sani, muna inganta asibitin koyarwa na Yeriman Bakura zuwa asibitin koyarwa mai nagartattun kayan aikin kiwon lafiya.
“Muna tattaunawa don samun fili a kusa don gina ɗakunan kwanan ɗalibai don jin daɗin ɗaliban mu.
“Game da batun biyan diyyar filaye kuwa, mun dage sosai wajen magance wannan matsalar. Mai ba da shawara na musamman kan ababen more rayuwa zai haɗa kai da hukumomin jami’o’i don nemo mafita.
“Game da wasu ayyuka da gwamnatocin baya suka fara, zan aika da wata tawaga domin tantance matsayinsu da sanin yadda za mu kammala su.
“Za mu bincika hanyoyin da za mu tallafa muku da kuɗaɗe. A kai, a kawo, al’ummarmu ne za su amfana domin makarantar tana Zamfara ne. Dole ne mu yi duk abin da za mu iya don ba da taimako ta kowane hali.
Tun da farko, Shugaban Jami’ar Tarayya ta Gusau, Rt. Hon. Aminu Sani Isah ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal bisa fimbin ayyukan da ya fara yi wa jami’ar tun kafin ya zama gwamnan Jihar Zamfara.

About andiya

Check Also

Dangote Hails Tinubu on Impact of Crude for Naira Swap Deal

      …As Dangote Refinery partners MRS to sell PMS at N935 per litre …

Leave a Reply

Your email address will not be published.