A wani gagarumin aikin sabunta birane, Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya bayyana cewa ayyukan gina tituna da ke gudana a faɗin jihar shaida ce ta yadda gwamnatinsa ke aiki tuƙuru wajen inganta harkar sufuri ta hanyar haɗa birane da ƙauyuka da ingantattun hanyoyi.
A ranar Laraba ne gwamnan ya ƙaddamar da aikin gina tituna mai tsawon kilomita 11.65 a garuruwan Rawayya, Furfuri, da Kurya Madaro a ƙananan hukumomin Bungudu da Ƙauran Namoda.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewe, kamfanin Bauhaus Global Investment Nigeria Limited ne aka bai w kwangilar aikin titin mai tsawon kilomita 11.65 a kan Naira Biliyan 6.6.
Sanarwar ta ƙara da cewa, ana sa ran kammala aikin cikin watanni 12 kacal.
A lokacin da yake ƙaddamar da aikin gina titin, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa, rashin samar da ababen more rayuwa a karkara da birane ya taimaka matuƙa wajen rashin ci gaban jihar.
Ya ce, “Rashin samar da ababen more rayuwa a karkara ya yi matuƙar tasiri wajen taƙaita harkokin noma da kasuwanci da kuma kawo cikas ga rayuwar mazauna karkara.
“Wannan aikin shaida ne a kan ƙudirin gwamnatinmu na inganta harkar sufurin mu ta hanyar haɗa birane da ƙauyukanmu da ingantattun hanyoyi. Ya yi daidai da ajandar ci gaban ababen more rayuwa, wanda ke da nufin samar da yanayi mai kyau ga ’yan kasuwa don bunƙasa harkokin su da magance matsalolin tsaro.
“Muna ganin gina ababen more rayuwa na birane da karkara a matsayin wani muhimmin hanyar ci gaba. Muna sha’awar ƙirƙirar tushe mai ƙarfi don ci gaba mai ɗorewa da bunƙasa tattalin arziƙi a kowane fanni.
“Baƙi da sauran al’ummar jihar Zamfara, ina so in yi amfani da wannan dama domin in ƙara tabbatar muku da irin jajircewar da gwamnatina ke yi wajen ci gaba da ƙoƙarin inganta jiharmu gaba ta kowane fanni na rayuwar ɗan Adam. Wannan shi ne aikina na a matsayin shugaban jiharmu, nauyi ne da Allah cikin hikimarSa Ya ɗora min.
“Da waɗannan kalamai kuma cikin alfahari nake ƙaddamar da aikin gina titi mai tsawon kilomita 11.65 a garuruwan Rawayya, Furfuri, da Kurya Madaro.”